Katsina, Daura za su samu asibitin koyarwa da FMC

Katsina, Daura za su samu asibitin koyarwa da FMC

- Gwamnatin jihar Katsina ta bayyana cewa za a habbaka cibiyar lafiya na tarayya zuwa asibitin koyarwa domin samar da ingantaciyyar kiwon lafiya ga mutane

- Masari yace gwamnatinsa na aiki tare da hukumomin tarayya domin mayar da babban asibitin Daura zawa cibiyar lafiya na tarayya wato Federal Medical Centre (FMC)

- Gwamnan yace za a dauki wannan matakin ne domin samar da ingantaccen kiwon lafiya ka mutane sannan kuma magance matsalolin

Gwamna Aminu Bello Masaraki na jihar Katsina ya bayyana cewa za a habbaka cibiyar lafiya na tarayya zuwa asibitin koyarwa domin samar da ingantaciyyar kiwon lafiya ga mutane.

Ya bayyana cewa gwamnatin jihar tana kuma aiki tare da hukumomin tarayya domin mayar da babban asibitin Daura zawa cibiyar lafiya na tarayya wato Federal Medical Centre (FMC).

Masari yayi Magana ne a fadar Galadiman Daura da na sarkin Maiadua, Ahmed Dadiri Ahmed a lokacin ci gaba da kamfen dinsa a yankin Daura.

Katsina, Daura za su samu asibitin koyarwa da FMC
Katsina, Daura za su samu asibitin koyarwa da FMC
Asali: Facebook

Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta mayar da babban asibitin Daura zuwa ginin cibiyar Maiadua mai kusan shekaru 30 wanda aka gina shi lokacin da yake a matsayin kwamishinan ayyuka na jiha a karkashin tsohon gwamna Saidu Barda.

KU KARANTA KUMA: Buhari, Atiku da sauransu za su sake shiga wata yarjejeniya

A cewarsa za a dauki wannan matakin ne domin samar da ingantaccen kiwon lafiya ka mutane sannan kuma magance matsalolin lalacewar gine-gine sakamakon rashin jajirtaccen shugabanci a mafi yawancin matakai na gwamnati.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng