Magoya bayan PDP 2,509 sun sauya sheka zuwa APC a Katsina

Magoya bayan PDP 2,509 sun sauya sheka zuwa APC a Katsina

- Mambobin jam’iyyar PDP 2,509 sun sauya sheka zuwa jam’iyyar APC a jihar Katsina

- Gwamna Aminu Masari ne ya tarbi masu sauya shekar a Sandamu lokacin kamfen dinsa a yankin

- Masari ya bayyana tarin ayyukan ci gaba da gwamnatinsa ta kaddamar a fadin jihar

Rahotanni sun kawo cewa akala mambobin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), 2,509 suka sauya sheka a ranar Litinin, 28 ga watan Janairu zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a karamar hukumar Sandamu da ke jihar Katsina.

Gwamna Aminu Masari ne ya tarbi masu sauya shekar a Sandamu lokacin kamfen dinsa a yankin.

Yace gwamnatinsa za ta fara aikin gyaran babban asibitin Sandamu da gyara hanyoyin garin a fadin sassa goma sha daya na yankin nan ba da jimawa ba.

Magoya bayan PDP 2,509 sun sauya sheka zuwa APC a Katsina

Magoya bayan PDP 2,509 sun sauya sheka zuwa APC a Katsina
Source: UGC

Masari ya bayyana cewa gwanatinsa ta yi ayyukan ci gaba da dama ciki harda hanyar kilomita 40 na Fago- Katsayal- Kwasarawa-Jirdede-Koza.

KU KARANTA KUMA: Zabe: Ku zabi shugaba mai gaskiya da rikon amana - Sheikh Bala Lau

Ya kuma bayyana cewa hanyoyin sun hade aruruwa a yankin da kuma na karamar hukumar Maiadua.

Gwamnan ya ara da cewa gwamnatinsa ta kuma sabonda hanyar Sandamu-Baure- Babban Mutum na tsawon kilomita 75 da kuma rijiyyin ruwa 150.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Shafin Naij.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel