An kama jami’an INEC na bogi su 3 suna diban ma’aikata na wucin-gadi

An kama jami’an INEC na bogi su 3 suna diban ma’aikata na wucin-gadi

- Rundunar yan sanda ta kama wasu jami’an INEC na bogi su 3 suna diban ma’aikata na wucin-gadi

- An bayyana sunayensu a matsayin Kaiyewu Folahan, Akintunde Ibukun da Azeez Kazeem

- An kuma gurfanar da masu laifin a gaban kotun Majistare, Yaba kan laifin, sojan gona, zamba, damfara da mallakar kayayyakin INEC ba bisa ka’ida ba

An kama wasu mutane uku a jiya a Yaba, jihar Lagas yayinda suke kokarin diban wasu jama’a a matsayin ma’aikatan wucin gadi na hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) na bogi.

Rundunar yan sanda ta bayyana wadanda aka kama a matsayin Kaiyewu Folahan, Akintunde Ibukun da Azeez Kazeem.

Kayayyakin da aka samu daga hannunsu a cewar yan sanda sun hada da, kwamfutar-tafi-da-gidanka, fam din diban ma’aikata na INEC Lagas guda 511 da hotunan fasfot a jiki.

Jami’in hulda da ama’a na rundunar yan sandan jihar Lagas, Chike Oti yace kamun ya biyo bayan wani korafi daga mataimakin daraktan INEC, a karamar hukumar Shomolu, Misis S.O. Akinwunmi, a ranar 22 ga watan Janairu cewa wasu mutane a shago mai lamba 33, Aluta Plaza, Federal College of Education, Akoka, na yi wa ma’aikatan INEC sojan gona sannan suna diban ma’aikatan wucin gadi.

An kama jami’an INEC na bogi su 3 suna diban ma’aikata na wucin-gadi
An kama jami’an INEC na bogi su 3 suna diban ma’aikata na wucin-gadi
Asali: Depositphotos

Oti yace bayan samun korafin, sai kwamishinan yan sandan jihar, Edgal Imohimi ya umurci ami’in dan sanda sashin ofishin yan sandan Pedro day a shiga sansanin mutanen tare da wasu jami’a. Hakan yayi sanadiyar kama su.

KU KARANTA KUMA: Ba zan yi sata ba, kuma ba zan bari kowa yayi sata ba – Buhari

Ya kara da cewa an gurfanar da masu laifin a gaban kotun Majistare, Yaba kan laifin, sojan gona, zamba, damfara da mallakar kayayyakin INEC ba bisa ka’ida ba.

Yace an garkame mutanen uku a gidan yari zuwa lokacin da za su cika ka’idar belinsu. An dage shari’an zuwa ranar 6 ga watan Afrilu, 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng