Ba kudinku Atiku ke so ba – Titi Abubakar ga yan Najeriya

Ba kudinku Atiku ke so ba – Titi Abubakar ga yan Najeriya

- Uwargidan dan takarar Shugaban kasa na jam’iyyar, Titi Abubakar, ta bayyana cewa mijinta Atiku ba kudin yan Najeriya yake so ba

- Titi tace mai gidan nata nada abun hannun shi sun ishe sa

- Ta bukaci yan Najeriya da su zabi mijinta domin abubuwa su daidaita

Uwargidan dan takarar Shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Titi Abubakar, ta bayyana cewa mijinta Atiku ba kudin yan Najeriya yake so ba saboda yana da nashi kudin.

Titi ta yi furucin ne a ranar Alhamis, 31 ga watan Janairu lokacin da take Magana a wani gangami a Abuja, jaridar The Nation ta ruwaito.

Ba kudinku Atiku ke so ba – Titi Abubakar ga yan Najeriya
Ba kudinku Atiku ke so ba – Titi Abubakar ga yan Najeriya
Asali: UGC

Ta bukaci yan Najeriya da su zabi mijinta domin abubuwa su daidaita, cewa Atiku na da shirin kawo karshen matsaloli da rashin aiki a kasar saboda shi mai samar da ayyuka ne.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buhari ya umarci da a zabi Ganduje a matsayin Gwamnan Kano a zaben 2019

A halin da ake ciki mun ji cewa wani tsohon mataimakin kwanturola na hukumar Fursuna na Najeriya, Alhaji Umaru Yari Sifawa, da wasu yan PDP 6441 sun sauya sheka zuwa APC a ranar Laraba, 30 ga watan Janairu.

Hakan na kunshe ne a wani jawabi dauke da sa hannun mai ba Sanata Aliyu Magatakarda Wammako shawara a kafofin watsa labarai, Bashir Rabe Mani, Dan Masanin Mani zuwa ga manema labarai a Sokoto.

Jawabin ya bayyana cewa sabbin masu sauya shekar sun samu tarba a APC daga hannun Shugaban jam’iyyar a jihar, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko a lokacin kamfen dinta a garuruwan Yabo da Bodinga, hedkwatan Yabo da kuma karamar hukumar Bodinga da ke jihar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel