Ka fadawa duniya kadarorin da ka mallaka – Afenifere ga Buhari

Ka fadawa duniya kadarorin da ka mallaka – Afenifere ga Buhari

- Kungiyar Yarbawa ta Afenifere ta yi kira ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya kaddamar da kadarorinsa duniya ta sani

- Afenifere ta ce lallai ya kamata Shugaban kasar ya zama abun koyi ta hanyar kaddamar da kadarorinsa

- A cewar kungiyar ta hake ne yan Najeriya za su tabbatar da gaskiyarsa da kuma tsayuwarsa akan kalamunsa

Kungiyar Yarbawa ta Afenifere a jiya, Talata, 29 ga watan Janairu ta yi kira ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya kaddamar da kadarorinsa duniya ta sani.

A wani jawabi daga Shugaban kungiyar, Cif R F Fasoranti, kungiyar ta ce lallai ya kamata Shugaban kasar ya zama abun koyi ta hanyar kaddamar da kadarorinsa cewa “don yan Najeriya su dauke shi a matsayin mutum mai kaifi daya a maganarsa."

Ka fadawa duniya kadarorin da ka mallaka – Afenifere ga Buhari

Ka fadawa duniya kadarorin da ka mallaka – Afenifere ga Buhari
Source: Depositphotos

Hakan martani ne ga dakatar da Shugaban alkalan Najeriya, Walter Onnoghen da Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi inda haan ya haifar da cece-kuce a kasar.

KU KARANTA KUMA: Atiku ya kai kara US, UK, EU, ya lissafo zunuban Buhari

A cewar kungiyar idan har Shugaban kasar ya kaddamar da kadarorin nasa hakan zai tabbatar da jajircewarsa a yaki da rashawar da yake yi.

Kungiyar ta ce ana gane shugaba nagari ne ta hanyar koyi da halaye nagartattu da yake muradi yaga mutanensa nayi

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Shafin Naij.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel