Matan Hausawa da Yarbawa a Ebonyi sun tsayar da Atiku a zabe mai zuwa

Matan Hausawa da Yarbawa a Ebonyi sun tsayar da Atiku a zabe mai zuwa

- Kungiyoyin mata daga kabilu daban-daban a kasar wadanda ke da zama a jihar Ebonyi sun marawa Atiku Abubakar baya

- Sun zargi gwamnatin tarayya karkashin APC da gaza cika alkawaran zaben da ta daukar ma yan Najeriya a fannin ababen more rayuwa, tsaro da kuma samar da aikin yi

- Shugabar kungiyar matan jihar Benue a Ebonyi, Ujoh Rose, ta ce gwamnatin APC ta yi watsi da mata a lamuranta

Kungiyoyin mata daga kabilu daban-daban a kasar wadanda ke da zama a jihar Ebonyi sun marawa tsohon mataimakain shugaban kasa, Atiku Abubakar baya gabannin zaben kasar mai zuwa.

Jaridar Leadership ta rahoto cewa matan sun bayyana a ranar Litinin, 21 ga watan Janairu cewa gwamnatin tarayya karkashin APC ta gaza cika alkawaran zaben da ta daukar ma yan Najeriya a fannin ababen more rayuwa, tsaro da kuma samar da aikin yi.

Matan Hausawa da Yarbawa a Ebonyi sun tsayar da Atiku a zabe mai zuwa

Matan Hausawa da Yarbawa a Ebonyi sun tsayar da Atiku a zabe mai zuwa
Source: Depositphotos

Matan sun bayyana matsayarsu ne a ofishin abokan Atiku da ke Abakaliki lokacin da suka kai ziyarar ban girma ga jagoran kungiyar a jihar, Linus Abaa Okorie.

KU KARANTA KUMA: Mambobin APC sun bawa hammata iska a harabar wata kotun tarayya

Da take Magana a madadin sauran mutanen, shugabar kungiyar matan jihar Benue a Ebonyi, Ujoh Rose, ta yi watsi da abunda ta bayyaa a matsayin rashin kula da mata a karkashin gwamnatin APC, cewa lokaci yayi da za a kawo karshen lamarin.

Ta bayyana cewa ba a tafiya da mata a lamuran gwamnatin nan saboda ikirarin cewa kamata yayi mata su kasance a ‘dayan dakin’.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel