Ba zan yi sata ba, kuma ba zan bari kowa yayi sata ba – Buhari
- Shugaban kasa Buhari ya sake jadadda alwashin da ya dauka na kin satar daga baitul malin kasar da kuma hana sauran mutane aikata hakan
- Buhari yace yan Najeriya za su iya bayar da shaidar cewa gwamnatinsa ta yi kokari sosai a wajen tattalin kudaden jama’a
- Ya ce sun samu gagarumin nasara a wajen ingnata tsaro, tattalin arziki da kuma yaki da cin hanci da rashawa
Shugaban kasa Muhammadu Buhari a jiya Laraba, 23 ga watan Janairu a Sokoto ya sake jadadda alwashin da ya dauka na kin satar daga baitul malin kasar da kuma hana sauran mutane aikata hakan.
Buhari ya sake ba yan Najeriya tabbacin cewa ba zai taba sata daga arzikinsu ba sannan kuma ba zai taba bari wani ya sace makomar kasar ba.

Asali: Facebook
Shugaban kasar yayi Magana a filin wasa na Giginya, wajen da aka gudanar da kamfen din neman tazarcensa a jiya, inda ya kara da cewa yan Najeriya za su iya bayar da shaidar cewa gwamnatinsa ta yi kokari sosai a wajen tattalin kudaden jama’a.
A cewarsa lokacin da ya ke kamfen din neman kuri’u a 2015, ya mayar da hankali, akan rashin tsaro, tattalin arziki da kuma yaki da cin hanci da rashawa, wanda ya kaddamar da gwamnatin tarayya a karkashin sa tayi matukar kokari.
KU KARANTA KUMA: INEC ta diba ma’aikatan wucin gadi 814,453 domin zabe
Akan nasararsa wajen yakar cin hanci da rashawa, Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa ta samu gagarumar nasara sannan tana ci gaba da jajircewa wajen yaki da rashawar.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT
Asali: Legit.ng