Ikuku: Rahama Sadau Ta Yi Ta'aziyyar Rasuwar Jarumin Fim a Najeriya

Ikuku: Rahama Sadau Ta Yi Ta'aziyyar Rasuwar Jarumin Fim a Najeriya

  • 'Yan fim a Najeriya na cigaba da jimamin rasuwar jarumi, Alex Ekubo da aka bayyana cewa rayuwarsa ta kare a ranar Talata, 12 ga Mayun 2026
  • Fitacciyar jarumar Kannywood, Rahama Sadau ta shiga cikin wadanda suka yi jimamin rasuwar Alex Ekubo, inda ta masa kyakyyawar shaida
  • Sauran jaruman fim a Najeriya sun bayyana alakar da suka yi da Ekubo, musamman irin rayuwar da ya yi tare da su kafin ya koma gidan gaskiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Masana’antar fim ta Nollywood a Najeriya ta shiga cikin yanayin baƙin ciki bayan samun labarin rasuwar ɗan wasan kwaikwayo Alex Ekubo, wanda aka fi sani da Ikuku.

Bayan labarin rasuwarsa ya fara yaɗuwa, an cika kafafen sada zumunta da saƙonnin ta’aziyya a ranar Talata, musamman Instagram da X, inda abokan aikinsa suka bayyana shi a matsayin mutum mai kirki da ladabi.

Kara karanta wannan

Alex Ekubo: Fitaccen jarumin fina finan Najeriya ya mutu yana da shekaru 40

Rahama Sadau da Alex Ekubo
Rahama Sadau tare da marigayi Alex Ekubo. Hoto: @Rahma_sadau
Source: Twitter

Rahoton da BBC ta wallafa ya nuna cewa jarumin ya rasu yana da shekara 40 a duniya bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.

Saƙon Rahama Sadau kan Ekubo

A wani sako da ta wallafa a X, jarumar Kannywood, Rahama Sadau ta nuna matukar damuwa kan rasuwar Ekubo, inda ta bayyana cewa yana da hali na gari.

Sadau ta ce jarumin ya kasance yana mutunta kowa a duk lokacin da ya ke mu'amala da mutane, dalilin da ta ce zai yi wahala a manta da shi.

Ta kara da cewa tana cigaba da tuno abubuwan da suka yi tare da suka hada da dariya, wasannin barkwanci kafin Allah ya masa rasuwa.

Rahama Sadau ta ce:

"Za a riƙa kewar ka har abada.
"Zan ci gaba da girmama ka,".
Jarumin fim, Alex Ekubo
Jarumi, Alex Ekubo da ya rasu. Hoto: Rahama Sadau
Source: Facebook

Ta'aziyyar sauran jaruman fim

Mai kamfanin EbonyLife Group, Mo Abudu ta tuna yadda Alex ke kiran ta da suna na musamman domin girmma ta tare da nuna baƙin ciki kan saƙon ƙarshe da ta tura masa amma bai samu ya karanta ba.

Kara karanta wannan

Jonathan ya amsa kiran 'yan Najeriya, zai tsaya takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP

Ta ce:

“Na tuna ka yi tafiya a bara ka kuma yi martani ga saƙo na bayan ka dawo. Na sake tura maka wani saƙo, amma ba ka samu damar mayar da amsa ba.
"Ban taɓa tunanin ba za a sake samun dama ba. Alex, za a yi kewarka sosai. Ka kasance mutum mai ƙaunar jama'a, mai gaskiya, mai kirki, kuma mai matuƙar girmama mutane a duk lokacin da muka yi aiki tare.”

Punch ta wallafa cewa jaruma Kate Henshaw ta tuna yadda Ekubo ya tsaya mata lokacin rasuwar mahaifiyarta shekaru biyu da suka wuce.

Ta ce:

“Mun yi hira lokacin da na lura ba ka cika amfani da kafafen sada zumunta ba, ka ce kana lafiya. Na so in samu damar rama alherin da ka yi mini a baya, Alex.”

'Yar fim, Halima Sabuwa ta rasu

A wani labarin, kun ji cewa an sanar da rasuwar jarumar Kannywood, Halima Sabuwa bayan doguwar rashin lafiya da ta yi a Kano.

Kara karanta wannan

Dan damfara ya sace wa mahajjaciya 'yar Najeriya daloli a Madina

Kwanaki kafin rasuwar ta, ta fito a wani bidiyo tana neman taimakon jama'a saboda rashin lafiya da talauci da ta ce ya mata katutu.

Jaruman fim da sauran mutane da dama a jihar Kano da ma wasu jihohin Najeriya sun yi jimamin rasuwar jarumar, suna rokon Allah ya jikanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng