Wata sabuwa: Majalisar Kano ta bude sabon shafin binciken sarki Sanusi II
- Majalisar dokokin jahar Kano ta bude sabon shafin binciken Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi
- Hakan ya biyo bayan wasu korafe-korafe da wasu mazauna jahar suka gabatar a gaban majalisar dokokin, inda suke zargin sa da ci wa al’adun garin fuska
- Shugaban majalisar dokokin, Abdulaziz Gafasa ya mika korafin ga kwamitin majalisar ta yi bincike cikin mako guda
Majalisar dokokin jahar Kano ta bude sabon shafin binciken Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi, kan wasu korafe-korafe da wasu mazauna jahar suka gabatar a gabanta, inda suke zargin sa da ci wa al’adun garin fuska.
Shugaban kwamitin jahar kan kananan hukumomi da masarautu, Zubairu Hamza-Masu ya bayyana a zauren majalisar cewa kwamitin ya karbi korafe-korafe biyu, daya daga wani Muhammad Muktar, sannan na biyun daga Shugaban hukumar KSPCE, Muhammad Bello-Abdullahi.
Dukkaninsu su biyun suna zargin Sarkin da wofantar da al’adun iyaye da kakanni na jahar da kuma rashin martaba masarautar.
Hamza ya ce dukkanin masu korafin na neman majalisar da ya zurfafa bincike kan zargin da suka gabatar mata.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buhari ya rantsar da Yemi Esan a matsayin sabuwar shugabar ma’aikatan tarayya
Shugaban majalisar dokokin, Abdulaziz Gafasa ya mika korafin ga kwamitin majalisar ta yi bincike cikin mako guda.
A wani labari na daban, mun ji cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya mika sakon ta'aziyya ga Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II bisa rasuwar kawunansa, Ambasada Ado Sanusi, Dan Iyan Kano.
Buhari, cikin sanarwar da mai magana da yawunsa Garba Shehu ya fitar ya bayyana bakin cikinsa bisa rasuwar Ambasaddan.
Ya kuma mika saƙon ta'aziyyarsa ga iyalan mamacin, Gwamnatin jihar Kano da mutanen jihar baki ɗaya a kan abinda ya kira "babban rashi na dattijo mai nagarta kuma ma'aikacin gwamanti da ya yi aiki tuƙuru."
"Ya bayyana marigayin a matsayin wakili na gari kuma uban ƙasa da ya yi ƙasarsa da garinsa hidima yadda ya dace."
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng