Yanzu Yanzu: Buhari ya rantsar da Yemi Esan a matsayin sabuwar shugabar ma’aikatan tarayya
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da Folashade Yemi Esan a matsayin sabuwar Shugaban ma’aikatan tarayya
- An yi bikin rantsarwar ne a yau Laraba, 4 ga watan Maris a fadar shugaban kasa da ke Abuja
- Hakan ya kasance ne kafin zaman majalisar zartarwa na mako
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da Folashade Yemi Esan a matsayin sabuwar Shugaban ma’aikatan tarayya a ranar Laraba, 4 ga watan Maris.
An yi bikin rantsarwar Esan wacce ta karbi mulki daga hannun Winifred Ekanem Oyo Ita yan mintoci kadan kafin fara zaman majalisar zartarwa na mako.
An gudanar da taron ne a zauren majalisar zartarwa na fadar Shugaban kasa, jaridar The Nation ta ruwaito.
Karin hotuna daga taron:
A baya mun ji cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari a daren Juma'a ya amince da murabus din Misis Winifred Ekanem Oyo-Ita a matsayin shugaban ma'aikatan gwamnatin tarayya daga ranar Alhamis 27 ga watan Fabrairun 2020.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Al’umman Damboa sun tsere yayin da yan Boko Haram ke musayar wuta da sojoji
Bayan haka, shugaban kasar ya kuma tabbatar da nadin Dakta Folashade Yemi-Esan wacce ta kasance shugaban ma'aikatan tarayyar na wucin gadi a matsayin tabbataciyar shugaban ma'aikatan gwamnatin tarayya (HoCSF).
Sakataren gwamnatin tarayya, Mista Boss Mustapha ne ya sanar da hakan a madadin sakataren dindin na na ofishin GSO, na ofishin sakataren gwamnatin tarayya, Mista Olusegun Adekunle kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Hakan na zuwa ne watanni biyar bayan an dakatar da Oyo-Ita daga kujerarta a kan zargin aikata rashawa.
An dakatar da Oyo-Ita daga kujerar ta ne a ranar 18 ga watan Satumban 2019 bayan da aka mika wani rahoton zargin ta da hannu cikin bayar da wasu kwangila daga ofishinta ba bisa ka'ida ba.
A cewar sanarwa na amincewa da murabus din nata, Shugaba Buhari ya ce za a cigaba da binciken zargin da ake mata na hannu cikin aikata rashawar. Shugaban kasar ya yi mata godiya bisa aikin da ta yi wa kasar ta kuma ya yi mata fatan alheri a ayyukan da za ta yi a gaba.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng