Shugaban hukumar hana yaduwar cutuka a Najeriya ya kebe kansa bayan ziyarar da ya kai China

Shugaban hukumar hana yaduwar cutuka a Najeriya ya kebe kansa bayan ziyarar da ya kai China

Shugaban hukumar hana yaduwar cutuka a Najeriya (NCDC), Chikwe Ihekweazu ya shiga sahun killace kansa na tsawon kwanaki 14 wanda shine tsarin daukar mataki.

Jaridar TheCable ta ruwaito cewa tuni ya shafe kwanaki bakwai zuwa yanzu.

Osagie Ehanire, ministan lafiya, ya bayyana a ranar Talata yayin da yake yiwa majalisar dattawa Karin bayani kan ayyukan ma’aikatarsa don hana yaduwar cutar Coronavirus a kasar cewa ya shiga tsarin kebe kansa ne saboda kwanan nan ya dawo daga kasar China.

“WHO ta aika wata tawaga na musamman zuwa China sannan ta yi magana da masani kimiya su yi duba ga abubuwan da ke haddasa wa sannan su yi kokarin fahimtar cutar sosai, da halayyar cutar. An gano cewa mutane da cutar ya kashe sun kasance wadanda ke dauke da wasu cututtuka irin su: tarin TB, kansa da kuma HIV,” in ji shi.

“Taron ya hada da matasa da manya. Daga cikin wadanda aka zaba harda Darakta Janar na hukumar NCDC. Muna alfahari sosai sannan cewa an shine dan Afrika daya tilo da aka karrama cikin kwararru. Sun je chan tsawon kimanin kwanaki tara.

"Mun rigada sun kafa dokoki a nan cewa duk mutumin da ya je China zai dauki matakin killace kansa. Chikwe ya je kuma ya dawo. Ya yi gwaji, baya dauke dashi amma muka ce dole zai ya shiga halin killace kai na kwanaki 14 wanda shine dalilin da yasa baya nan. Ba a yarda ya fito ba har sai bayan kwanaki 14. Saboda idan ka kafa doka, ya zama dole ka bi."

Shugaban hukumar hana yaduwar cutuka a Najeriya ya kebe kansa bayan ziyarar da ya kai China
Shugaban hukumar hana yaduwar cutuka a Najeriya ya kebe kansa bayan ziyarar da ya kai China
Asali: UGC

Wata majiya ta NCDC ta tabbatar da cewa Ihekwehazu na killace a gidansa amma ta ki bayyana wajen.

A wani labarin kuma, mun ji cewa Shugaban hukumar hana yaduwar cutuka a Najeriya, NCDC, Dakta Chikwe Ihekweazu ya yi watsi da ikirarin tsohon shugaban hukumar zabe ta kasar Farfesa Maurice Iwu na cewa ya gano maganin cutar Coronavirus.

Dakta Chikwe ya bayyana cewa babu yadda za a yi a gano magnanin cutar da ba ta dade da billa ba a duniya, shafin BBC ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Karancin albashi: Babu yadda za a yi na iya bugo kudi – Gwamnan Gombe ya yi korafi

Ya ce sabuwar cuta ce kuma ba a taba sanin da ita ba ko a fannin lafiya, sai watanni biyu da suka gabata, kuma ya ce kafin a gane tasirin maganin dole sai an gwada kan marasa lafiya, wanda da yawansu a China suke.

Farfesa Iwu dai ya yi ikirarin gano maganin cutar ta numfashi ne, wadda ta kashe fiye da mutum 3,000 a fadin duniya, inda kuma kasarsa Najeriya ta kasance cikin kasashen da cutar ta bulla.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel