Manyan APC na dumi yayinda ake kishin-kishin Sanata Ajimobi zai zama Shugaban rikon kwarya na jam’iyyar

Manyan APC na dumi yayinda ake kishin-kishin Sanata Ajimobi zai zama Shugaban rikon kwarya na jam’iyyar

Tsige Adams Oshiomhole daga matsayin Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da babbar kotun tarayya tayi ya jefa jam’iyyar a matsalar shugabanci.

An tattaro cewa ga dukkan alamu tsohon gwamnan jahar Oyo, Sanata Isiaka Ajimobi wanda aka sanar da zamowarsa mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa a ranar Laraba, 4 ga watan Maris ka iya zama Mukaddashin shugabanta.

Bisa ga kundin tsarin mulkin APC na 2010 kamar yadda aka gyara, mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa na Kudu ne zai rike kambun mulkin jam’iyyar a matakin rikon kwarya.

Manyan APC na dumi yayinda ake kishin-kishin Sanata Ajimobi zai zama Shugaban rikon kwarya na jam’iyyar
Manyan APC na dumi yayinda ake kishin-kishin Sanata Ajimobi zai zama Shugaban rikon kwarya na jam’iyyar
Asali: Facebook

A wani jawabi daga Lanre Isa-Onilu, a daren ranar Laraba, ya bayyana cewa wani zama da kwamitin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar suka gudanar a ranar 14 ga watan Janairu 2020, sun yanke shawarar amincewa da tsohon gwamnan jahar Oyo, Sanata Ajimobi a matsayin sabon mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa, daga Kudu.

Sai dai kuma an tattaro cewa akwai wasu runduna a jam’iyyar da ka iya bijirewa sabon lamarin.

KU KARANTA KUMA: Tsaro da lantarki sun sa Jihohin Arewa maso Gabas za su gana a Jihar Gombe

A halin da ake ciki, mun ji cewa majalisar zartarwa watau NEC ta jam’iyyar APC ta na tunanin yadda za ta maye gurbin Adams Oshiomhole a matsayin shugaban jam’iyya.

Jaridar ta ce tun a Ranar Laraba wasu gwamnonin jihohin APC su ka fara neman wanda zai canji Adams Oshiomhole wanda kotu ta dakatar, kuma aka hana shi shiga ofishinsa a Abuja.

Ana sa ran cewa za a kira taron NEC na gagagwa, a wannan taro ne za a samu matsaya har a fito da wanda zai cigaba da shugabantar jam’iyya. A halin yanzu APC ba ta da shugaba.

Majiyar ta bayyana cewa akwai yiwuwar manyan jam’iyyar su bukaci Oshiomhole ya yi murabus, sannan sai a nada shugaban jam’iyya na rikon kwarya kafin a kai ga tabbatar da shi.

Sai dai Adams Oshiomhole ta bakin Mai magana da yawunsa, Simon Ebegbulem, ya bayyana cewa ya shigar da kara a kotu, ya na kalubalantar wannan hukunci da aka yanke jiya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel