'Yan bindiga sun kashe Hakimi da wani mutum guda a Zamfara

'Yan bindiga sun kashe Hakimi da wani mutum guda a Zamfara

Rahotanni sun kawo cewa yan bindiga sun kashe mutum biyu a wani hari da suka kai kan al’umman kauyen Kujemi a masarautar Dansadau da ke karamar hukumar Maru na jahar Zamfara.

Kakakin yan sandan jahar Zamfara, SP Muhammad Shehu ya tabbatar da faruwar lamarin.

Shehu yayin da yake tabbatar da lamarin a wani jawabi a ranar Litinin, ya bayyana cewa wadanda aka kashen sune hakimin kauye da wani mutum guda biyo bayan harin da yan bindiga suka kaddamar a ranar Lahadi da misalin karfe 8:40 na dare.

'Yan bindiga sun kashe Hakimi da wani mutum guda a Zamfara

'Yan bindiga sun kashe Hakimi da wani mutum guda a Zamfara
Source: UGC

Dan sandan ya ci gaba da bayyana cewar yan bindigan sun je garin su da yawa sannan suka kai hari kauyen inda suka kashe Malam Gambo na kauyen Karauchi da Mustapha Halilu na yankin Dansadau.

A cewar Shehu bayan Yan sandan sun samu labarin, sai aka shirya tawagar hadin gwiwa na jami’an Operation Puff Adder da sojoji sannan aka tura su zuwa yankin don dakile ci gaban harin da kuma kama masu laifin.

KU KARANTA KUMA: Ba na nadamar datse min hannu da shari'a ta yi - Dan jihar Zamfara

A wani labarin kuma, mun ji cewa wasu 'yan bindiga da ba san ko su wanene ba a daren ranar Litinin sun kai hari a garin Bagwai da ke karamar hukumar Bagwai ta jihar Kano inda suka kashe mutane biyu tare da raunata wasu mutanen hudu.

The Nation ta gano cewa wadanda ake zargin 'yan bindigan ne sun isa garin ne a cikin mota misalin karfe 10.30 na dare inda suka kashe dan wani jigo a jam'iyyar PDP a garon da wata shugaban shiyya na PDP a Kano ta Arewa, Hajiya Balaraba Sani.

An kuma gano cewa sun kashe wani matashi mai suna Muhammad dan shekara 35 ma'aikacin sashin lafiya na karamar hukumar Bagwai yayin harin.

Majiyar ta ce lamarin ya faru ne a gaban shagon wasu masu sayar da kifi a garin inda mutane ke taruwa su shakata.

An bayyana cewa daga bisani 'yan sanda sun iso sun kwashe gawarwakin da wadanda suka jikkata zuwa asibiti.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel