Muna iya sake duba kasafin kudin 2020 saboda coronavirus – Zainab Ahmed

Muna iya sake duba kasafin kudin 2020 saboda coronavirus – Zainab Ahmed

Ministar kudi, Zainab Ahmed ta bayyana cewa akwai yiwuwar sake duba kasafin kudin kasar don yi mata kwaskwarima sakamakon cutar coronavirus.

Majalisar dokokin kasar dai ta aiwatar da kasafin kudin 2020 na naira tiriliyan 10.59 a ranar 5 ga watan Disamba, 2019, sannan Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya mata hannu a ranar 17 ga watan Disamba.

An aiwatar da kasafin kudin ne bisa ga farashin danyen main a dala 57 kowace ganga tare da karfin samar da gangar mai miliyan 2.1 a kowace rana.

Muna iya sake duba kasafin kudin 2020 saboda coronavirus – Zainab Ahmed
Muna iya sake duba kasafin kudin 2020 saboda coronavirus – Zainab Ahmed
Asali: Twitter

Amma a yanzu cutar wanda ya yadu a kasashe 64, ya shafi farashin danyen mai, wanda shine babban hanyar samun kudaden shigar Najeiya.

Ministar ta ce zuwa yanzu dai cutar ta shafi yanayin tattara kudin harajin kasar da kuma farashin gangar man fetur, wanda ke kasa da yadda suka kiyasta a kasafin kudin.

Ta bayyana hakan ne ga manema labarai jim kadan bayan kammala zaman majalisar zartarwa a ranar Laraba, 4 ga watan Maris.

"Dama can muna da niyyar sake duba kasafin kudi tun lokacin da aka saka hannu kan dokar kasafin," in ji ministar.

Ta kara da cewa: "Abin da muke kokarin yi shi ne, idan mu ka ga kudaden haraji sun yi kasa sosai to dole ne mu yi wa kasafin kudin kwaskwarima ta hanyar rage shi.

"Yanzu haka muna hako ganga miliyan 2 ta danyen mai amma yakan kai 2.1 a wasu lokuta. Wannan ma wata garkuwa ce.

KU KARANTA KUMA: Manyan APC na dumi yayinda ake kishin-kishin Sanata Ajimobi zai zama Shugaban rikon kwarya na jam’iyyar

"Duka dai ba ma daukar wasu matakai a yanzu har sai mun samu lokacin da ya dace sannan mu yi gyara kan kasafin ta hanyar hadin gwiwa da majalisun tarayya."

A wani labari na daban, mun ji cewa Hukumar ICPC mai yaki da Barayi da masu satar dukiyar gwamnati ta ce ta gano wasu makudan kudi da ta ke zargin an sace daga asusun gwamnatin Najeriya.

A cewar jaridar kasar nan ta The Nation, ICPC ta bayyana cewa ta na zargin an sace wadannan dukiya ne daga shekarar 2016 zuwa shekarar bara watau 2019.

Hukumar ta ce ta karbo kudin ne daga hannun tsofaffin ma’aikatan da su ka yi wa gwamnatin Najeriya aiki a karkashi hukumomi da ma’aikatun da ake da su.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel