Dangote, BUA sun kara farashin buhun siminti a Najeriya, yanzu ya haura N12,500

Dangote, BUA sun kara farashin buhun siminti a Najeriya, yanzu ya haura N12,500

  • Farashin buhun siminti mai nauyin kilo 50 ya haura zuwa N13,000 a wasu sassan Najeriya, lamarin da ya ƙara jefa masu gine-gine cikin matsin tattali
  • Dillalan siminti sun koka kan yadda kamfanoni irinsu Dangote, BUA ke ci gaba da sauya farashi, abin da ke kawo cikas ga kasuwancin su
  • Masana tattalin arziki sun buƙaci gwamnatin tarayya ta bai wa ƙarin kamfanoni lasisin shigo da siminti domin samar da gasa da rage tsadar kaya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - ‘Yan Najeriya na ci gaba da kokawa kan tashin farashin siminti bayan da farashin buhun siminti mai nauyin kilo 50 ya kai har N13,000 a wasu kasuwannin kasar nan.

Sabon farashin ya biyo bayan karin da manyan kamfanonin samar da siminti irin su Dangote da BUA suka yi a baya-bayan nan.

Kara karanta wannan

Yahudawa sun bankawa masallaci, motoci wuta yayin ibada a Isra'ila

'Yan kasuwa sun sauya farashin siminti zuwa N1300
Wani mutumi yana daukar buhun siminti. Hoto: Novatis via Getty Images
Source: Getty Images

An kara farashin siminti a Najeriya

Lamarin ya kara jefa masu gine-gine, ‘yan kwangila, masu gidaje da masu shirin ginawa cikin matsin tattali sakamakon tsadar kayan gini, kamar yadda jaridar Legit,ng ta ruwaito.

Dillalan siminti da masu rarraba kaya sun bayyana takaicinsu kan yadda ake ci gaba da kara farashin siminti akai-akai.

Sun ce hakan na jawo musu matsaloli wajen gudanar da kasuwanci tare da haddasa rikici tsakaninsu da kwastomomi.

Wani dillali da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa ya yi odar buhunan siminti 50 tun watan Janairu a kan farashin N11,000 kowanne.

Sai dai lokacin da ya je karbar kayan a watan Mayu, an bukace shi da ya biya sabon farashin N13,000 kan kowanne buhu kafin a ba shi kayan.

Masu gine-gine sun shiga matsala

Dillalin ya ce sabon karin ya dagula shirinsa tare da tilasta masa neman karin kuɗi domin kammala aikinsa.

Ya ce:

Kara karanta wannan

Uwargida ta cinna wa kishiyarta da ƴaƴanta 2 wuta a Kano, bayanai sun fito

“Na yi odar kayan tun farko ne domin guje wa irin wannan matsala, amma da na dawo karba sai aka ce dole in cika kudi in saya a sabon farashi.”

Masu gine-gine da dama sun bayyana cewa yawan tashin farashin siminti na rage musu karfin ci gaba da ayyukan gini.

Masana tattalin arziki sun ce bai kamata a bar ‘yan Najeriya a hannun wasu ‘yan tsirarun kamfanoni da ke sarrafa farashin siminti ba.

Yan kasuwa sun fadi abin da ya jawo farashin siminti ya haura 12,500.
Buhun siminti na kamfanin Dangote, da wani d'an kasuwa yana magana da 'yan jarida. Hoto: Bloomberg/Contribtutor
Source: Getty Images

Masana sun yi gargadi kan tsadar siminti

Wani masanin tattalin arziki, Osas Igho, ya bayyana cewa bude kasuwa ga karin masu shigo da siminti zai samar da gasa tare da rage tsadar kaya.

A zantawarsa da jaridar Legit.ng, Osas Igho ya ce:

"Tsarin da ake da shi yanzu ya bai wa wasu tsirarun manyan kamfanoni damar kayyade farashi yadda suke so ba tare da wata matsala ba.
"Hakan na ci gaba da kara jefa masu amfani da siminti cikin wahala musamman a wannan lokaci da tsadar rayuwa ke ƙaruwa a Najeriya.
"Akwai bukatar gwamnatin tarayya ta bai wa ƙarin kamfanoni lasisin shigo da siminti domin samar da gasa da rage tsadar kaya."

Kara karanta wannan

Gwamnatin Zamfara ta magantu da ake zargin harin jirgi ya kashe yan kasuwa 100

Farashin simintin Dangote, BUA

A wani labari, mun ruwaito cewa, farashin buhun siminti ya tashi a sassan Najeriya wanda hakan ya tsayar da ayyukan gine-gine da dama a Fabrairun 2026.

Masu sayar da siminti a Legas suna zargin dillalai da tsawwala farashin simintin alhalin suna sayo shi da araha daga kamfani.

A birnin Abuja da jihar Kwara farashin siminti ya haura N11,000 da Legit Hausa ta jero farashin simintin kamfanonin Dangote da BUA.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com