Yanzu Yanzu: Kotu ta dakatar da Oshiomhole daga matsayin Shugaban APC
- Wata babbar kotun birnin tarayya a Jabi, Abuja ta dakatar da Adams Oshiomhole daga matsayin Shugaban jam’iyyar APC na kasa
- Alkalin kotun, Justis Danlami Senchi, a ranar Laraba, 4 ga watan Maris, ya umurci Oshiomhole da ya sauka zuwa lokacin da za a yanke hukunci
- An dai shigar da wata kara ne inda aka bukaci kotu da ta tsige Oshiomhole daga matsayin shugaban APC
Wata babbar kotun birnin tarayya a Jabi, Abuja ta dakatar da Adams Oshiomhole daga matsayin Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa.
Justis Danlami Senchi, a ranar Laraba, 4 ga watan Maris, ya umurci Oshiomhole da ya sauka zuwa lokacin da za a yanke hukunci kan karar da ce neman a tsige shi daga matsayin Shugaban APC na kasa.
Zuwa yanzu dai babu cikakken labari kan rahoton.
A baya mun ji cewa shugaban jam’iyyar APC mai mulki Adams Oshiomhole ya na fuskantar kalubale bayan gwamnonin jam’iyyar sun shiga cikin masu taso sa.
Jaridar tace idan aka tafi a haka, kwanakin Adams Oshiomhole a matsayin shugaban jam’iyya na kasa su na daf da zuwa karshe har an fara tunanin zai iya rasa mukaminsa a farkon shekarar 2020.
Hakan na zuwa ne bayan da aka fara jin kishin-kishin cewa wasu daga cikin gwamnonin APC sun bi zugar da ke neman ganin bayan shugaban jam’iyyar. Yanzu dai Oshiomhole ya na kan siradi.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buhari ya rantsar da Yemi Esan a matsayin sabuwar shugabar ma’aikatan tarayya
Majiyar Jaridar ta Daily Sun tace abin da ya ke ceton Oshiomhole a wannan lokaci kurum shi ne sa bakin da fadar shugaban kasa ta yi a cikin rikicin. A wani bangare, an musanya wannan jita-jita.
Rahotanni sun ce gwamnonin za su nemi a tsige Oshiomhole muddin ya ki bin hanyar lalama ya ajiye aikin da kansa. Sai dai Hadimin shugaban jam’yyar, Simon Ebegbulem ya karyata wannan.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng