Karancin albashi: Babu yadda za a yi na iya bugo kudi – Gwamnan Gombe ya yi korafi

Karancin albashi: Babu yadda za a yi na iya bugo kudi – Gwamnan Gombe ya yi korafi

Gwamnan jahar Gombe, Muhammad Yahaya, ya koka kan rashin iya biyan ma’aikata N30,000 a matsayin mafi karancin albashi da gwamnatinsa ta kasa.

Gwamnan wanda aka yiwa tambayoyi a wani shirin Channels TV na News Night ya ce babu yadda za a yi ya iya buga kudi a kokarinsa na biyan bukatun ma’aikatan.

“Lamarin kamar na ko ina ne. Namu ya fi muni a matsayin jaha, idan kuka duba teburin kudaden shiga, Gombe ce ta biyun kusa da karshe.

“Ina ganin muna saman Nasarawa da Ekiti be kawai ko kuma ma muyi daidai. Babu yadda za a yi na iya buga kudi na zo na ba mutane,” in ji shi.

Karancin albashi: Babu yadda za a yi na iya bugo kudi – Gwamnan Gombe ya yi korafi
Karancin albashi: Babu yadda za a yi na iya bugo kudi – Gwamnan Gombe ya yi korafi
Asali: UGC

Gwamnan ya yi ikirarin cewa gwamnatocin baya, musamman wacce ta gama ba ta damu da karancin albashi ba.

Yahaya wanda ya zargi tsohon Gwamna Ibrahim Dankwambo da aiwatar da manyan ayyuka ya ce bai mayar da hankali kan lamuran da suka shafi mutanen jahar ba.

Da yake magana kan kudaden shiga, gwamnan ya bayyana cewa jahar na samun naira miliyan 300 duk wata, inda ya kara da cewa ta dogara ne a kan kudaden da gwamnatin tarayya ke bata duk wata.

KU KARANTA KUMA: Imo: Kotun koli ta yi watsi da bukatar sake duba hukuncin kwace kujerar gwamnan PDP

Sai dai kuna ya bayyana gurbataciyyar jagoranci da ayyuka marasa inganci a matsayin babban abunda ya haddasa rashin samun kudaden shiga yadda ya kamata.

A wani labari na daban, mun ji cewa Kungiyar SSANU ta manyan Ma’aikatan Jami’a ta bayyana cewa har yanzu su na kan tsarin tsohon albashi ne a Najeriya duk da karin da gwamnati ta yi tun kwanaki.

Kamar yadda mu ka samu labari, SSANU ta bayyana cewa rashin fara dabbaka sabon tsarin albashi a kan ‘Yan kungiyarta ya jefa su cikin matsin kudi da kuma tattali.

Kungiyar ta ce ba za ta iya bada tabbacin zaman lafiya a makarantun jami’an gwamnatin tarayya muddin aka cigaba da daukar lokacin ba tare da an kara masu albashin ba.

SSANU ta yi wannan jawabi ne a Ranar Litinin ta bakin Mai magana da yawunta, Mista Salaam Abdussobur. A cewarsa an manta da kungiyar a karin albashin da aka yi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel