Oshiomhole ya yi wani nadi da baya bisa ka’ida bayan kotu ta dakatar dashi – Jigon jam’iyyar

Oshiomhole ya yi wani nadi da baya bisa ka’ida bayan kotu ta dakatar dashi – Jigon jam’iyyar

Mataimakin Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa (arewa maso gabas), ya ce Shugaban jam’iyyar, Adams Oshiomhole, na neman haddasa Karin matsaloli.

Wata babbar kotun tarayya a ranar Laraba, 4 ga wata Maris ta dakatar da Oshiomhole daga matsayin Shugaban jam’iyyar na kasa.

Da yake jawabi ga manema labarai a ranar Laraba, Mustapha ya ce jim kadan bayan kotun ta yanke hukuncin dakatar da Oshiomhole, sai shi (Oshiomhole) ya umurci Lanre Isa-Onilu, kakakin jam’iyyar da ya yi jawabi don sanar da Waziri Bulama a matsayin mukaddashin sakataren jam’iyyar na kasa.

Oshiomhole ya yi wani nadi da baya bisa ka’ida bayan kotu ta dakatar dashi – Jigon jam’iyyar
Oshiomhole ya yi wani nadi da baya bisa ka’ida bayan kotu ta dakatar dashi – Jigon jam’iyyar
Asali: UGC

Dama dai Mustapha da Oshiomhole sun raba gari kan zabar Bulama a matsayin sakataren jam’iyyar.

Mataimakin Shugaban jam’iyyar, wanda ya goyi bayan hukuncin kotu na dakatar da Oshiomhole, ya ce nadin Bulama da ya yi baya bisa ka’ida.

Da aka tambaye shi ko zai amince da zabar Bulama a matsayin sakataren jam’iyyar na kasa idan jam’iyyar ta yarda da wannan matsayar, Mustapha ya ce, “jam’iyyar ba za ta iya amincewa da Bulama ba, wacece jam’iyyar? Dole Mutumin da zai riki wannan matsayar ya kasance babban mutum a jam’iyyar.”

KU KARANTA KUMA: Hukumar yaki da rashawa ta Kano ta aika sammaci ga Sarki Sanusi

A halin da ake ciki, mun ji cewa majalisar zartarwa watau NEC ta jam’iyyar APC ta na tunanin yadda za ta maye gurbin Adams Oshiomhole a matsayin shugaban jam’iyya.

Jaridar ta ce tun a Ranar Laraba wasu gwamnonin jihohin APC su ka fara neman wanda zai canji Adams Oshiomhole wanda kotu ta dakatar, kuma aka hana shi shiga ofishinsa a Abuja.

Ana sa ran cewa za a kira taron NEC na gagagwa, a wannan taro ne za a samu matsaya har a fito da wanda zai cigaba da shugabantar jam’iyya. A halin yanzu APC ba ta da shugaba.

Majiyar ta bayyana cewa akwai yiwuwar manyan jam’iyyar su bukaci Oshiomhole ya yi murabus, sannan sai a nada shugaban jam’iyya na rikon kwarya kafin a kai ga tabbatar da shi.

Sai dai Adams Oshiomhole ta bakin Mai magana da yawunsa, Simon Ebegbulem, ya bayyana cewa ya shigar da kara a kotu, ya na kalubalantar wannan hukunci da aka yanke jiya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng