Ban yi danasanin barin Ganduje saboda Kwankwaso ba – Dungurawa

Ban yi danasanin barin Ganduje saboda Kwankwaso ba – Dungurawa

Wani tsohon hadimi na musamman ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jahar Kano kan kawata birane, Hashim Sulaiman Dungurawa, ya ce bai yi danasanin yasar da tsohon ubangidansa da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ba saboda Sanata Rabiu Kwankwaso da jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Dungurawa ya yi murabus daga matsayin hadimin Ganduje a watan Maris din shekarar da ya gabata kafin sake zaben gwamna a jahar, cewa an kayar da tsohon ubangidan nasa a zaben.

A wata hira da manema labarai a Abuja, Dungurawa ya ce ya yi murabus daga matsayinsa sannan ya bar jam’iyyar APC domin ya kare mutuncinsa.

Ban yi danasanin barin Ganduje saboda Kwankwaso ba – Dungurawa

Ban yi danasanin barin Ganduje saboda Kwankwaso ba – Dungurawa
Source: UGC

“Ba zan iya yiwa gwamnati mai rashawa da bata kare ra’ayin jaha da mutanenta aiki ba. Duba ga halin da ake ciki zuwa yanzu, ya gaza mana kuma ban yi danasanin komawa tafiyar Kwankwasiyya da PDP ba.

“Mun rasa zabe a matsayin gwamnati mai mulki da tazarar sama da kuri’u 20,000 amma Ganduje ya kasa karban kaddarar Allah. Na gwammaci na kasance a nan saboda na san a zaben 2023, Za mu yi waje da su kuma sannan za mu gani idan Za su yarda da hakan ko a’a,” in ji shi.

KU KARANTA KUMA: Harin Kaduna: Gwamnonin Arewa su farka daga barci ko kuma a wayi gari babu yankin – Shehu Sani

Kan tafiyar Kwankwasiyya, Dungurawa ya ce ta yi fice har wajen Najeriya. “Muna samun gayyata daga kasashen da ke makeabtaka kan mu je mu mara masu baya da dabarunmu,” in shi.

A wani labarin kuma mun ji cewa, Tsohon gwamnan jahar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bara game da zargin da ake yi masa da hannu cikin badakalar kudin makamai a zamanin da yake minista, sa’annan ya wanke manyan hadimansa guda biyu, Injiniya Abba Kabir Yusuf da Abdullahi Umar Ganduje.

A makon nan ne wasu rahotanni daga jaridu daban daban suka bayyana cewa hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta kaddamar da bincike a kan badakalar kwangilar sayo makamai da aka yi a ma’aikatar tsaro a shekarar 2008.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel