Yanzu Yanzu: Al’umman Damboa sun tsere yayin da yan Boko Haram ke musayar wuta da sojoji

Yanzu Yanzu: Al’umman Damboa sun tsere yayin da yan Boko Haram ke musayar wuta da sojoji

Rahotanni sun kawo cewa a yanzu haka Damboa, hedkwatar wata karamar hukuma a jahar Borno na karkashin harin yan ta’addan Boko Haram.

Mazauna yankin sun ce yan ta’addan sun zo su da yawa da misalin karfe 6:30 na safiyar ranar Laraba, 4 ga watan Maris sanan suka fara harbi ba kakkautawa, jaridar TheCable ta ruwaito.

Daya daga cikin mazauna yankin ya ce sama da sa’a daya, sojoji daga rundunar soji ta brigade 25 a Damboa na ta musayar wuta da yan ta’addan.

“Sun zo su da yawa a motocin hilux. Mun gan su kimanin su 20 kafin muka fara gudu cikin daji,” daya daga cikin mazauna yankin da suka tsere.

Yanzu Yanzu: Al’umman Damboa sun tsere yayin da yan Boko Haram ke musayar wuta da sojoji

Yanzu Yanzu: Al’umman Damboa sun tsere yayin da yan Boko Haram ke musayar wuta da sojoji
Source: Facebook

“Sun zo a rukuni biyu. Daya sun shigo ta arewacin Sambisa saan sauran ta Alagaruno.

“Sojoji daga rundunar bataliya ta 25 sun zo kimanin mintuna 30 sannan har yanzu, sama da sa’a guda, suna ta musayar wuta da yan ta’addan.”

Harin na zuwa ne kwana guda tal bayan yan ta’addan sun kai hari Bwalakila, wani kauye da ke makwantaka dasu a karamar hukumar Chibok.

Wani mazaunin kauyen ya bayyana cewa sojojin bataliya ta 117 sun dakile harin a Chibok, amma cewa sun riga da sun sace kayayyakin abinci daga wajen mazauna kauyen da suka far mawa.

Sai dai ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar, Sagir Musa ba kan harin Damboa.

Wani soja daga bataliyan ya bayyana cewa dakarun soji a tsaron yankin yayinda suke samun tallafi daga rundunar sojin sama.

KU KARANTA KUMA: Najeriya ba za ta san zaman lafiya ba har sai talaka ya zama wani ba tare da ya san kowa ba - Ndume

“An turo wani jirgin yaki daga rundunar a Maiduguri,” in ji shi.

“Don haka a yanzu muna da tallafi daga rundunar sojin sama, kuma muna kora makiyan dga wajen da kuma kare yankin. Wasun su na nan har ynzu amma mun rage karfinsu a yanzu.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel