Coronavirus: Jami’an NCDC sun tantance ministocin Buhari kan tsoron cutar (hotuna)

Coronavirus: Jami’an NCDC sun tantance ministocin Buhari kan tsoron cutar (hotuna)

Biyo bayan gano cutar coronavirus a Lagas, jami’an hukumar NCDC sun tantance wasu mambobin majalisar Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba, 4 ga watan Maris.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa an gudanar da shirin tantancewar ne a matsayin matakin hana yaduwar cutar ta COVID-9 wanda aka fi sani da conavirus.

Legit.ng ta rahoto cewa haka zalika an tantance wasu ma’aikatan fadar Shugaban kasa da bakin da ke shiga fadar.

Coronavirus: Jami’an NCDC sun tantance ministocin Buhari kan tsoron cutar (hotuna)
Coronavirus: Jami’an NCDC sun tantance ministocin Buhari kan tsoron cutar (hotuna)
Asali: UGC

A cewar rahoton an fara tantancewar na daya-bayan-daya a ranar Talata, 3 ga watan Maris, inda ake duba karfin zafi ko sanyi na jikin ma’aikata da baki kafin su shiga ofishoshinsu.

Sai dai an kara binciken ne a ranar Laraba, 4 ga watan Maris, wanda shine ranar zaman majalisar zartarwa da rantsar da Folasade Yemi-Esan a matsayin shugabar ma’aikatan tarayya bayan Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da ita.

KU KARANTA KUMA: Yanzun-nan: APC ta ce za ta bi umurnin kotu kan Oshiomhole

Rahoton ya kuma bayyana cewa an tantance ahli da bakin da suka zo shaida bikin rantsarwar a kofar shiga fadar Shugaban kasa tare da basu abun wanke hannu kafin aka bari suka shiga zauren majalisa zartarwar a Abuja.

A wani labarin kuma, mun ji cewa Kungiyar kiwon Lafiya ta duniya WHO ta shawarci jama’a da su rinka amfani da naurorin zamani wajen bukatunsu na kudi, domin kudi kan iya jawo yaduwar coronavirus.

Cutar Coronavirus zata iya zama akan kudi na tsawon kwanaki, Kungiyar kiwon lafiya tayi gargadi a daren Litinin.

Cutar Coronavirus zata iya yaduwa ta hanyar abubuwan da suke dauke da cutar da kuma haduwa da wadanda suke dauke da cutar, cewar kungiyar WHO.

Bankin Kasar Ingila ta gano cewa kudi kan iya daukar kananan kwayoyin cuta, kuma ta karfafa akan yawan wanke hannaye.

A watan baya, bankin kasar Koriya da China sun fara tsaftacewa da killace kudaden da akayi amfani dasu domin takaita yaduwar annobar cutar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel