Hukumar yaki da rashawa ta Kano ta aika sammaci ga Sarki Sanusi

Hukumar yaki da rashawa ta Kano ta aika sammaci ga Sarki Sanusi

- Hukumar sauraron korafe-korafen jama’a da yaki da cin hanci da rashawa ta jahar Kano, ta aika sammaci ga Sarkin Kano Muhammad Sanusi

- Hukumar ta bukaci Sarki Sanusi da ya gurfana a gabanta a ranar Alhamis domin ci gaba da amsa tambayoyi kan zargin almubazaranci da naira biliyan 3.4 da masarautar Kano karkashin jagorancinsa ta yi

- Da yake tabbatar da gayyatar, wani babban jami’in hukumar ya ce an ba basaraken sa’a 24 ya gurfana a gaban hukumar

Hukumar sauraron korafe-korafen jama’a da yaki da cin hanci da rashawa ta jahar Kano, ta gayyaci Sarkin Kano Muhammad Sanusi, kamar yadda majiyoyi suka bayyana.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa hukumar ta bukaci Sarki Sanusi da ya gurfana a gabanta a ranar Alhamis domin ci gaba da amsa tambayoyi kan zargin almubazaranci da naira biliyan 3.4 da masarautar Kano karkashin jagorancinsa ta yi.

Wata majiya ta fadar ta bayyana cewa sarkin ya samu wasikar gayyata daga wajen hukumar yaki da rashawar.

Hukumar yaki da rashawa ta Kano ta aika sammaci ga Sarki Sanusi
Hukumar yaki da rashawa ta Kano ta aika sammaci ga Sarki Sanusi
Asali: Twitter

Da aka tambaye shi ko Sanusi zai amsa gayyatar, majiyar ta ce: “B azan iya tabbatar da wannan ba, amma kun san cewa Sarki Sanusi mutum ne mai bin dokar kasa.”

Da yake tabbatar da gayyatar, wani babban jami’in hukumar ya ce an ba basaraken sa’a 24 ya gurfana a gaban hukumar.

“Zan iya tabbatar maku da cewar babu ja da baya a bincikensa da majalisar masarautar,” in ji jami’in wanda baya so a ambaci sunansa.

A baya mun ji cewa Majalisar dokokin jahar Kano ta bude sabon shafin binciken Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi, kan wasu korafe-korafe da wasu mazauna jahar suka gabatar a gabanta, inda suke zargin sa da ci wa al’adun garin fuska.

Shugaban kwamitin jahar kan kananan hukumomi da masarautu, Zubairu Hamza-Masu ya bayyana a zauren majalisar cewa kwamitin ya karbi korafe-korafe biyu, daya daga wani Muhammad Muktar, sannan na biyun daga Shugaban hukumar KSPCE, Muhammad Bello-Abdullahi.

KU KARANTA KUMA: Manyan APC na dumi yayinda ake kishin-kishin Sanata Ajimobi zai zama Shugaban rikon kwarya na jam’iyyar

Dukkaninsu su biyun suna zargin Sarkin da wofantar da al’adun iyaye da kakanni na jahar da kuma rashin martaba masarautar.

Hamza ya ce dukkanin masu korafin na neman majalisar da ya zurfafa bincike kan zargin da suka gabatar mata.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel