Najeriya ba za ta san zaman lafiya ba har sai talaka ya zama wani ba tare da ya san kowa ba - Ndume

Najeriya ba za ta san zaman lafiya ba har sai talaka ya zama wani ba tare da ya san kowa ba - Ndume

Shugaban kwamitin majalisar dattawa kan rundunar soji, Sanata Ali Ndume, a jiya Talata ya koka kan rashin gaskiya da ake nunawa wajen daukar aiki a hukumomin gwamnatin tarayya, cewa ya zama dole a dauki hakan a matsayin laifi.

Ya ce talakawan Najeriya da dama basu samun aiki a hukumomin gwamnati saboda “nasu shamakin shine cewa basu san kowa ba.”

Ya ce Najeriya ba za ta san zaman lafiya ba “har sai wanda yake ba dan kowa ba ya zama Wani ba tare da sanin kowa ba.”

Najeriya ba za ta san zaman lafiya ba har sai talaka ya zama wani ba tare da ya san kowa ba - Ndume
Najeriya ba za ta san zaman lafiya ba har sai talaka ya zama wani ba tare da ya san kowa ba - Ndume
Asali: Facebook

Ndume ya bayyana hakan yayin da yake jawabi ga manema labarai kan dokar jami’ar sojoji a Biu, jahar Borno, wacce ta kai matakin karatu na biyu a zauren majalisar dattawa.

Ya ce koda dai suma masu neman aiki a wasu lokutan su kan biya cin hanci saboda sun matsu, cewa wannan hali ba bai kyau bane sannan cewa ya kamata a haramta hakan.

“Idan za su dauki mutane aiki, toh ya zamana an dauke su bisa tsarin kundin tsarin mulkin tarayya da cancanta.

“Bana jin dadi kan hakan saboda na samu damar zama abun da nake a yau ba tare da sanin kowa ba. Yanzu akwai wasu mutane iri na, amma nasu shamakin shine basu san kowa ba."

A wani labari na daban, mun ji cewa wata kungiya ta ‘Yan kishin kasa a Najeriya, ta yi magana gama da salon nadin mukaman gwamnatin tarayya da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ke jagoranta.

KU KARANTA KUMA: Malami: Har yanzu ba a dawowa Gwamnatin tarayya da kudin satar Abacha ba

Wannan kungiya ta yi tir da yadda shugaban kasar ya ke raba mukamai inda ta zargin gwamnatinsa da nunawa mutanen Kudu maso Gabas banbanci da wariya.

Shugaban wannan kungiya da kuma Sakatarensa, Okonkwo James da Isa Pai, su ne su ka yi magana a gaban ‘Yan jarida a cikin farkon makon nan a birnin tarayya Abuja.

Okonkwo James da Isa Pai sun zanta da ‘Yan jarida ne a sakamakon nada Misis Folasade Yemi-Esan da aka yi a matsayin sabuwar shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel