Ahmad Yusuf
11517 articles published since 01 Mar 2021
11517 articles published since 01 Mar 2021
Yan kabilar Ijaw sun gargaɗi shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu kan tsige Gwamna Siminalayi Fubara, sun yi barazanar cewa za su ba shi mamakin ta inda bai zato ba.
Gudauniyar Alhaji Aliko Ɗangote ta fara raba kayan abinci ga mabuƙata a faɗin kananan hukumomi 774 na Najeriya, za a raba buhunan shinkafa mai nauyin kilo 10.
Muƙaddashin shugabam PDP na kasa, Ambasada Umar Damagum ya bayyana cewa zaben da tsagin Wike suka shirya na shugabannin jam'iyya a Kudu maso Kudu ya saɓa doka.
Rahotanni daga yankin ƙaramar hukumar Kachia ta jihar Kaduna na nuna cewa mahara sun tashi mutanen garuruwa 5, sun sace wasu matasa a rugar fulani.
Tsohon gwamnan jihar Anambra kuma ɗan takarar shugaban kasa na LP a zaben da ya gabata na 2023 ya shiga ganawar sirri da Gwamna Bala Muhammed a Bauchi.
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai ya musanta raɗe-raɗin da ke yawo cewa rashin naɗa shi minista ne ya tunzura shi ya bar jam'iyyar APC.
Gwamna Siminalayi Fubara ya nuna damuwa kan hana shi shiga zauren Majalisar Dokokin Jihar Ribas na wucin gadi domin sakw gabatar da kasafin kuɗin 2025.
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya bayyana cewa ya gaya wa Buhari shirinsa na barin APC kuma sai da ya amince sannan ya koma SDP.
Rahotanni sun bayyana cewa jami'an tsaron da ke cikin ayarin Gwamna Babagana Umaru Zulum sun fatattaki ƴan Boko Haram da suka tare matafiya a Borno.
Ahmad Yusuf
Samu kari