Yan Binidga Sun ga Takansu, An Ceto Mutane 73 da Aka Sace Tare da Cafke Miyagu 175

Yan Binidga Sun ga Takansu, An Ceto Mutane 73 da Aka Sace Tare da Cafke Miyagu 175

  • Dakarun ƴan sanda sun samu nasarar ceto mutane 73 da aka yi garkuwa da su a faɗin jihar Katsina a watan Mayu, 2025
  • Ƴan sandan sun kuma kama waɗanda ake zargi da aikata laifuka daban-daban har mutum 175 a faɗin kananan hukumomin jihar Katsina
  • Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Katsina, Abubakar Sadiq ya ce an samu wannan nasarori ne da taimakon gwamnati da al'ummar Katsina

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Katsina - Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Katsina ta sanar da ceto mutane 73 da aka sace tare da kama mutane 175 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a fadin jihar.

Rundunar ƴan sandan ta bayyana cewa ta samu wannan nasara ne a cikin watan Mayu na shekarar 2025.

Yan sanda sun ragargaji masu aikata laifuka a Katsina.
Yan sanda sun ceto mutane 73, sun kama miyagu sama da 100 a Katsina Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar, Abubakar Sadiq, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, kamar yadda Channels tv ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan sanda sun kama miyagu 175 a Katsina

Sadiq ya ce wannan nasara ta kasance ɗaya daga cikin manyan ayyuka da nasarorin da rundunar ta cimma a watan da ya gabata a faɗin jihar Ƙatsina.

A cewarsa, daga cikin waɗanda aka kama akwai mutane 15 da ake zargi da hannu a ayyukan fashi da makami, mutum ɗaya a lamarin garuwa da mutane da wani da ya mallaki bindiga ba bisa ƙa'ida ba.

"An kama mutum 20 a laifin kisa, mutum 30 a laifin fyade da kuma mutane 108 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban,” in ji sanarwar.

An kwato mugayen makamai daga miyagu

Kakakin ƴan sanda ya kara da cewa dakarun sun kuma kwato makamai daga hannun miyagun waɗanda suka haɗa da bindiga AK-49 kirar gida, bindigar Revolver ƙirar gida da alburusai guda 506.

Sauran kayan da ƴan sanda suka kwato a watan Mayu sune babura biyu da ake zargin na sata ne da dabboɓi 174 da aka sace wa jama'a.

Abubakar Sadiq ya ƙara da cewa dakarun ƴan sanda sun samu waɗannan nasarorin ne da haɗin gwiwar gwamnatin jihar da ma al’ummar Katsina.

Sufetan yan sanda na kasa.
Yan sanda sun rage ƙarfin masu aikata miyagun laifuka a Katsina a watan Mayu Hoto: @PoliceNG
Asali: Facebook

Ƴan sanda sun gode da haɗin kan jama'a

Ya gode gwamnatin da duka jama'ar jihar Katsina bisa goyon baya da hadin kan da suke ba ƴan snada wajen tabbatar da zaman lafiya da hana aikata laifuka.

"Muna kuma bukatar karin goyon baya da hadin kai daga jama’a domin ci gaba da samun irin wannan nasara," in ji shi.

Abubakar ya kuma gode wa Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, bisa irin goyon bayan da yake bai wa rundunar, tare da yabawa Kwamishinan ‘Yan Sanda na Katsina, CP Bello Shehu.

Ƴan bindiga sun farmaki dakarun C-Watch

A wani labarin, kun ji cewa ƴan bindiga sun yi wa dakarun tsaron Katsina (C-Watch) kwanton ɓauna, sun kashe mutum.biyar daga ciki.

Maharan sun aikata wannan ɗanyen aiki ne a wani mummunan farmaki da suka kai ƙauyen Maharba da ke ƙaramar hukumar Matazu ta jihar Katsina.

Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya jagoranci wata babbar tawagar tsaro zuwa yankin a ranar Juma’a domin tantance ɓarnar da aka yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262