"Kamar Yana Raye," Abubuwan da Aka Ji Mabiyan Sheikh Masussuka na Fada a Wurin Jana'iza
- Dubban mabiya marigayi Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka sun yi dafifi a titunan Katsina yayin da ake kai shi makwancinsa na ƙarshe
- Rahotanni sun nuna cewa an gudanar da sallar jana'izarsa a babban masallacin Muhammad Dikko bayan sallar Juma'a
- An binne shi a makabartar Abbatuwa, kusa da abokinsa Adam Abubakar Nasarawa da aka kashe tare da shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Katsina - Dubban mabiya malamin addinin Musulunci da aka kashe, Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka, sun cika titunan birnin Katsina a ranar Juma'a yayin da aka yi jana'izarsa.
Mabiyan malamin sun rika ambatar wasu kalmomi cikin alhini suna cewa, “Masussuka bai mutu ba, kyawawan ayyukansa suna nan da rai; maƙiyansa sun ji kunya,” yayin da ake shirin birne gawarsa.

Source: Facebook
Leadership ta ruwaito cewa kalmar “Allahu Akbar” ta riƙa tashi daga cikin dandazon mutanen da suka taru, yayin da masu jimami ke ƙoƙarin ganin malamin a karo na ƙarshe.

Kara karanta wannan
Sojoji sun ceto mutane 70, sun kama ƙasurgumin ɗan bindiga da ya addabi mutane a Arewa
Wasu na zubar da hawaye a fili, yayin da wasu ke miƙa hannayensu domin taɓa motar asibitin da ke ɗauke da gawarsa.
Yadda aka gudanar da jana'izar
An gudanar da sallar jana'izar a fadar Mai Martaba Sarkin Katsina jim kaɗan bayan kammala sallar Juma'a. Limamin Babban Masallacin Muhammadu Dikko ne ya jagoranci sallar da misalin ƙarfe 2:59 na rana.
Yawan mutanen da suka halarta ya yi yawa matuƙa, lamarin da ya sa aka sha wahala wajen fitar da motar asibitin daga cikin dandazon jama'a.
Hakan ya sa tafiya zuwa makabarta domin birne gawar Sheikh Masussuka ta ɗauki sa'o'i da dama.
Imam Rasheed Masussuka, wanda ɗalibi ne kuma surukin marigayin, ne ya jagoranci jerin gwanon motocin da suka raka gawarsa zuwa makabartar Abbatuwa da ke cikin birnin Katsina.
A nan ne aka birne shi kusa da abokinsa, Adam Abubakar Nasarawa, wanda aka kashe tare da shi ranar Litinin a kofar gidan malamin da ke Dutsin-Ma.

Source: Facebook
Manyan baki sun halarci jana'izar
Jami'an tsaro da mambobin ƙungiyar sa-kai ta Yan Agaji sun yi ƙoƙarin shawo kan dandazon jama'a tare da tabbatar da zaman lafiya, yayin da masu jimami ke tururuwa domin shaida yadda ake gudanar da jana'izar.
Daga cikin waɗanda suka halarci jana'izar akwai Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, wakilan ƙungiyoyin addinin Musulunci na Tijjaniyya, Ƙadiriyya da Shi'a, da kuma fitattun malaman Musulunci daga ƙasashen Ghana, Jamhuriyar Nijar da Chadi.
Yan sanda sun fara farautar makasan Masussuka
Kun ji cewa ’yan sanda sun fara farautar wasu mutane biyu da ake zargi da kashe Sheikh Yahaya Masussuka da abokinsa, Adamu Abubakar, a haban gidan malamin da ke Dutsin-Ma.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, Ali Umar Fage, ya bayar da umarnin tura jami’an dabaru da na gudanar da ayyuka zuwa yankin domin kamo wadanda ake zargi da kashe malamin.
Kwamishinan ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan, abokansu, mabiyansu da al’ummar Dutsin-Ma bisa wannan rashi.
Asali: Legit.ng
