Shugaban INEC Ya Yi Maganar Goyon Bayan Wani ‘Dan Takara Zaben 2027
- Shugaban INEC ya ce hukumar sa ba ta da dan takara ko jam’iyyar da take goyon baya a zabe mai zuwa
- Ya sha alwashi hukumar da yake jagoranta za ta yi aiki bisa doka tare da tabbatar da zabe mai gaskiya da adalci
- Joash Amupitan ya shaida cewa masu rajistar zabe sun haura miliyan 103 kuma za a kada kuri’a ko ina a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Joash Amupitan ya ce hukumar INEC ba ta da wani ‘dan takara ko jam’iyya da ta fifita ko ta ke tare da ita a zabe mai zuwa.
Shugaban hukumar zaben ya tabbatar da INEC a matsayin adila wanda ba ta aiki da son rai wajen gudanar da zabe a Najeriya.

Source: Facebook
Kungiyar ECOWAS ta hadu da Shugaban INEC
Kamar yadda aka wallafa a Facebook, Joash Amupitan ya yi wannan bayani ne lokacin da ya karbi bakuncin ‘yan tawagar ECOWAS a Abuja.
Tsohon mataimakin shugaban kasar Sierra Leone, Victor Bockarie Foh ya jagoranci tawagar kungiyar zuwa wajen hukumar tarayyar.
A nan ya shaida wa kowa cewa INEC ta na duba irin tanadin da ta yi wa zabe kuma ya tabbatar da cewa ba za su yi wa kowa son kai ba.
Da yake magana ranar Juma’a, 30 ga watan Oktoba 2026, ya tabbatar da yana ran gadi da nufin ganin yadda aka shirya wa zaben badi.
"INEC a karkashina ba ta da wani ‘dan takara ko jam’iyyar siyasa.
"Tilon biyayyar mu tana ga dokar kasa, zabin ‘yan Najeriya masu kada kuri’a da kuma cigaban tsarin farar hula a kasarmu.
- Farfesa Joash Amupitan
Babu inda ba za a yi zabe a Najeriya ba
Farfesa Amupitan ya kuma ce za a kada kuri’a a rumfuna 8, 809 da ake da su a fadin kananan hukumomi 774 da suke kasar nan.
A jaridar Vanguard, an rahoto tsohon malamin jami'ar yana cewa mutanen da suke cikin rajistar hukumar INEC sun zarce miliyan 103.
Ganin watanni suka rage a fita zaben shugabanni, farfesan ya yi albishir da cewa an yi nisa wajen shirye-shirye jadawalin zabe a Najeriya.
Hukumar INEC ta ce kawo yanzu an kammala matakai uku na rajistar masu zabe kuma an gama wallafa rajistar farko na masu kada kuri’a.
Fasaha za ta yi aiki a zabe - INEC
Shugaban na INEC ya yi bayanin yadda za a yi amfani da na’urar BVAS wajen aikin zabe.
A kokarin ganin an gyara harkar, Amupitan ya ce an kawo tsarin zamani na amfani da eEC8A da zai taimaka wajen dura sakamako a IReV.
An ji shi yana yi wa tawagar ECOWAS din bayanin yadda hukumar zabe ta hada-kai da jami’an tsaro wajen ganin zabin mutane ya yi tasiri.
NDC tana jiran hukumar INEC a Kano
Da farko an cire sunan Aminu Abdussalam Gwarzo daga cikin jerin sunayen ’yan takarar gwamna a 2027 kamar yadda aka ji labari.
Jam’iyyar NDC ta shigar da ƙorafe-ƙorafe kan cire sunan da aka yi kuma yanzu an fahimci cewa akwai yiwuwar ya shiga takara
A wani kaulin kuma an ce rikicin kotu ya kawo wa NDC cikas, amma dai Husseini Mairiga ya fadi yadda suka yi da jami'an INEC.
Asali: Legit.ng


