Da Gaske Sojoji Sun Hamɓarar da Shugaban Ƙasa a Kamaru? Bincike Ya Bankaɗo Gaskiya
Cameroon - Wasu rahotanni sun fara yawo a kafafen sada zumunta cewa dakarun sojoji sun kifar da gwamnatin shugaban ƙasa, Paul Biya na ƙasar Kamaru.
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Rahotannin da ke yawo sun yi ikirarin cewa sojoji sun hamɓarar da gwamnatin Kamaru kuma ba ma a san inda Shugaba Paul Biya ya shiga ba ballantana halin da yake ciki.

Asali: Getty Images
Daga ina jita-jitar juyin mulkin ta faro?
A ranar Talata da ta wuce, wani shafin TikTok mai suna jimmoexpress37 ya wallafa bidiyo mai tsawon minti takwas da ke ikirarin cewa sojojin Kamaru sun karbe mulki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bidiyon ya samu masu kallo 41,200, tare da mutane 694 da suka tura wa abokansu, inda yawancin masu sharhi a sashin kwament ke tambayar yaushe irin haka zai faru a Najeriya.
A cikin bidiyon, an ji muryar namiji mai ƙarfin sauti yana bayyana yadda aka yi juyin mulkin, wadanda suka jagoranta da kuma yadda Kamaru ta samu 'yanci.
A cewar mai gabatar da rahoton, juyin mulkin ya samo asali ne daga gagarumin rashin amincewar jama'a da mulkin kama-karya na Shugaba Biya tsawon shekaru 41.
Ya kara da cewa ɓatan shugaban kasar na kusan wata biyu a lokacin da ya tafi jinya a kasashen waje a watan Satumban bara ya kara hura wutar fushin jama'a.
“Juyin mulkin ya faru ne da safe misalin karfe 5:00 na asuba,” in ji shi, yana mai yabawa yadda aka hamɓarar da gwamnatin Biya ba tare da zubar da jini ba.
Ya kwatanta shi da “tsabtaccen aiki na tiyata,'' sai dai bai fadi ranar da hakan ta faru ba.
A rubutun da ke bayan bidiyon, an ce:
“Sojoji sun kifar da Shugaban Kamaru, Paul Biya da karfe 5:00 na safe. Ba a zubar da jini ba, jama'a sun fara murna a Yaoundé.”
Bincike: Menene gaskiyar wannan rahoto?
The CableCheck ta gudanar da bincike ta amfani da fasahar zamani, kuma ta gano cewa daga cikin bidiyoyin da aka yi ikirarin sojoji sun kwace Kamaru akwai wanda aka wallafa ranar 8 ga Yuni.
Wani shafin YouTube mai suna Jeunesse Panafricaine, wanda ke da mabiya 2,7000 ne ya wallafa bidiyon.
A bayanin da ke jikin tashar YouTube din, ta ce suna goyon bayan jagororin soji irin su Kanal Assimi Goïta (Mali), Captain Ibrahim Traoré (Burkina Faso), da Janar Tchiani (Nijar).
Bincike ya nuna cewa ga dukkan alamu da fasahar AI aka yi amfani wajen ƙirƙira da sanya muryar da ke cikin bidiyon.
Ko da gaske an kifar da gwamnatin Biya?
A al’adance, idan an yi juyin mulki, ana cafke shugaban da aka hambarar da shi ko wasu mukarraban gwamnatinsa.
Sai dai shafin shugaban ƙasar Kamaru, Paul Biya na Facebook, bai daina aiki ba har zuwa lokacin da aka fitar da wannan rahoto.

Asali: Getty Images
A cikin wata sanarwa a ranar Alhamis, Shugaba Biya ya bukaci ‘yan kasar su dage wajen hada kai da ƙaunar juna.
"Mu kaucewa duk wani banbancin da muke da shi, mu tunkari manufofinmu, mu yi amfani da banbancin kabila da ra'ayoyi wajen cimma burinmu," in ji shi.
Bugu ƙari har yanzu babu wata jarida daga cikin jaridun Kamaru da ta fitar da rahoton juyin mulkin.
An daɗe ana yaɗa jita-jita game da lafiyar Shugaba Biya mai shekaru 91, tare da jingina masa mutuwa ko kuma yiwuwar kifar da gwamnatinsa.
A shekarar da ta gabata, lokacin da ya yi batan fiye da wata daya, aka baza jita-jita cewa ya mutu, amma gwamnati ta musanta hakan, ta kuma haramta wa kafafen yada labarai magana kan lafiyarsa.
Kammalawa
Ikirarin da ake cewa dakarun sojoji sun yi juyin mulki a ƙasar Kamaru ƙarya ne, babu wata kafa ta gwamnati ko jaridu a cikin kasar da ta tabbatar da hakan.
An shirya zaɓen shugaban ƙasa na gaba a Kamaru ranar 5 ga Oktoba, 2025, kuma ana sa ran Shugaba Paul Biya, wanda ke kan mulki tun 1982, zai sake tsayawa takara.
Sojoji sun kwace mulki a ƙasar Côte d’Ivoire?
A wani labarin, kun ji cewa rahoton da ke nuna an yi wa shugaban kasar Côte d’Ivoire, Alassane Ouattara, juyin mulki ba gaskiya ba ne.
Ana cikin yaɗa jita-jitar sai fadar shugaban ƙasa ta tabbatar da cewa Alassane Ouattara ya halarci wani muhimmin taro na majalisar ministoci ranar Laraba.
Daga cikin batutuwan da aka tattauna a taron akwai buƙatar faɗaɗa hanyoyin samar da wutar lantarki da kuma samar da gidaje masu inganci ga ƴan ƙasa.
Asali: Legit.ng