Kungiyoyin Kwadago Sun Kaure da Fada kan Shirin Tallafin N70,000 na Tinubu

Kungiyoyin Kwadago Sun Kaure da Fada kan Shirin Tallafin N70,000 na Tinubu

  • Shugaban NLC, Joe Ajaero, ya caccaki TUC kan ƙin amincewa da alawus ɗin sufuri na N70,000 da aka yi wa ma’aikata
  • Ajaero ya ce yarjejeniyar nasara ce, amma ya gargadi gwamnati kada ta dakatar da tallafin ba tare da sabon tsarin mafi ƙarancin albashi ba
  • Ƙungiyar NECA ta ce ba za a ɗaure ma’aikatan kamfanoni masu zaman kansu da yarjejeniyar albashi ba tare da shigarta tattaunawar ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya (NLC) ta caccaki takwararta, Ƙungiyar Ƙwadago ta TUC kan maganar tallafa wa ma'aikata.

NLC ta soki TUC ne bisa ƙin amincewa da alawus ɗin sufuri na N70,000 da aka cimmawa domin tallafa wa ma’aikata.

Kungiyoyin kwadago sun kaure da fada
Shugabannin kungiyoyin kwadago da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Nigeria Labour Congress HQ.
Source: Facebook

NLC ta bayyana muhimmancin yarjejeniyar da Tinubu

Shugaban NLC, Joe Ajaero, ya bayyana tallafin a matsayin muhimmiyar yarjejeniya da za ta rage wa ma’aikata raɗaɗin tashin farashin man fetur da tsadar rayuwa, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Obi ya fadi yadda zai yi aiki tare da Kwankwaso idan suka yi nasara a 2027

Ajaero ya kuma shawarci TUC da ta nemi wata yarjejeniya mafi alheri ga mambobinta maimakon sukar yarjejeniyar da ba ta shiga tattaunawarta ba.

NLC ta yaba da tallafi ga ma'aikata
Shugaban NLC, Joe Ajaero da yan kungiyarsa suna tattaki a Abuja. Hoto: Nigeria Labour Congress HQ.
Source: Facebook

Ajaero ya kare yarjejeniyar N70,000

Da yake magana a shirin Channels Television ranar Alhamis, Ajaero ya ce ma’aikata suna cikin wahala kafin gwamnati ta amince da wannan tallafi.

Ya ce:

“Ma’aikatan Najeriya suna cikin wahala, babu wani tallafi ko wani mataki da aka ɗauka. Mun matsa lamba ta hanyar barazanar shiga yajin aiki. Har mun kusa shiga yajin aikin domin samun wani tallafi, daga ƙarshe kuma aka ba mu wannan.”

Shugaban NLC ya bayyana yarjejeniyar a matsayin babbar nasara, musamman duba da halin da tattalin arzikin ƙasar yake ciki.

Da yake magana kan sukar da TUC ta yi, Ajaero ya nuna mamakinsa, yana mai cewa ƙungiyar ba ta shiga tattaunawar da aka yi ba wanda ya samar da sauki ga ma'aikata a Najeriya.

Kara karanta wannan

Jerin waɗanda ba za a turawa tallafin N70,000 duk wata a Najeriya ba

Ya ce:

“Daga yanzu zuwa watanni shida masu zuwa, wannan babbar nasara ce, ba TUC ce ta sanya hannu kan yarjejeniyar ba, kuma bai kamata ka soki wani abu da ba ka shiga tattaunawar da aka yi dominsa ba.
“Shawarata ita ce su je su nemi abin da ya fi wannan. Idan suna so, su nemi naira miliyan ɗaya.”

A cewarsa, yarjejeniyar za ta iya zama tubalin fara wasu tattaunawa domin inganta walwalar ma’aikata a sassa daban-daban.

NLC na son sabon mafi ƙarancin albashi

An ji cewa shugaban NLC, Joe Ajaero ya yi gargadin cewa bai kamata wa'adin watanni shida na biyan alawus ɗin ya ƙare ba tare da samar da sabon tsarin mafi ƙarancin albashi ba.

Ya ce sabon tsarin albashin ya kamata ya yi la'akari da tsadar sufuri, abinci, gidaje da sauran muhimman buƙatun rayuwa duba da yadda ma'aikata ke shan wahala a Najeriya.

Hakan ya biyo bayan halin matsi da aka shiga duba da cewa mafi karancin albashin N70,000 ba zai wadaci ma'aikaci ba a kowane mataki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.