Tsohon Ɗan Takarar Shugaban Kasa Ya Amince Zai Koma APC? Momodu Ya Yi Bayani

Tsohon Ɗan Takarar Shugaban Kasa Ya Amince Zai Koma APC? Momodu Ya Yi Bayani

  • Dele Momodu ya musanta raɗe-raɗin da mutane ke yaɗawa cewa ya gama shirin ficewa daga PDP zuwa jam'iyyar APC mai mulki
  • Fitaccen ɗan jaridar, wanda ya nemi takarar shugaban ƙasa har sau biyu ya ce ba zai taɓa sauya sheƙa zuwa APC ba saboda ba ta da manufofi masu kyau
  • Cif Momodu ya zargi gwamnatin APC da ɓuya a bayan dimokuraɗiyya, amma a zahiri tana tafiyar da mulkin kama karya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shahararren ɗan jarida kuma jigo a jam’iyyar PDP, Dele Momodu, ya ce ba shi da wani shiri na sauya sheka zuwa APC kamar yadda mutane ke yaɗawa.

Cif Momodu ya ce ya yanke shawarar ba zai shiga APC ba saboda irin salon mulkin danniya da rashin bin dokokin dimokuraɗiyya da yake zargin sun mamaye jam’iyya mai mulki.

Shahararren ɗan jarida kuma jigon PDP, Dele Momodu.
Delek Momodu ya musanta jita-jitar cewa yana shirin komawa APC Hoto: Dele Momodu
Asali: Facebook

Jigon PDP ya yi wannan furucin ne a wata hira da aka yi da shi a kafar talabijin ta Channels tv ranar Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dele Momodu na shirin komawa jam'iyyar APC?

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa ya ƙaryata jita-jitar cewa yana shirin sauya sheka zuwa APC, saboda rikice-rikicen cikin gida da PDP ke fuskanta.

Fitaccen ɗan jaridar ya ce:

"Ba zan taɓa komawa APC ba, bai kamata ana yawan surutu kan wannan lamarin ba, ya kamata mutane su yi watsi da jita-jitar.
"Da da gaske ina shirin shiga APC ai ba zan saki baki ina urutu kan abubuwan da ke faruwa a ƙasa ba, saboda haka babu wannan maganar, ina nan a PDP.

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar ya soki APC

Jigo a PDP kuma wanda ya tsaya neman takarar shugaban ƙasa sau biyu, ya caccaki salon shugabancin APC, inda ya ce jam’iyyar na tafiyar da mulki ne irin na kama-karya.

"Ba zan iya zama a wurin da mutun ɗaya kaɗai ke da ikon juya akalar dukka mutanen da suke tare da shi ba, duk gogewarsu da kwarewarsu, ya zama shi ne ubangidan kowa," in ji shi.

Momodu ya bayyana hakan ne a daidai lokacin da PDP ke fama da rikicin shugabanci da rabuwar kai, lamarin da ya sa ake ta hasashen wasu jiga-jigan jam’iyyar na shirin barinta.

Dele Momodu ya ce zama daram a PDP.
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa ya soki salon mulkin APC Hoto: Dele Momodu
Asali: Facebook

Momodu ya ce gangar jikinsa ta rage PDP

Sai dai ya bayyana cewa rashin gamsuwa da yadda PDP ke tafiya ba yana nufin goyon bayan APC ba ne, kamar yadda rahoton Leadership ya kawo.

Dele Momodu ya kara da cewa

“Gangar jikina na cikin PDP, amma raina ya riga ya bar jam’iyyar.”

A cewar wani tsohon shugaba a PDP ta karamar hukumar Ɗanja a Katsina, babbar jam'iyyar adawa na dab da rushewa ko kuma ta zama mara tasiri.

Shamsu Ahmad, wanda kwanan nan ya sauya sheka tare da ɗan Majalisar Bakori/Ɗanja, ya shaida wa wakilin Legit Hausa cewa ba abin da ya yi saura a PDP sai rigima.

"Bana tunanin za a iya gyara PDP nan kusa, cin amana ya yi yawa, yau zaku zauna domin kokarim gyara gobe za ku ji abin da kuka tattauna a wurin makiya.
"Alamu sun nuna PDP ta kama hanyar zama tarihi, shiyasa kowa ke gudunta," in ji shi.

Jigo a PDP ya yi barazanar komawa APC

A wani labarin, kun ji cewa tsohon kakakin kwamitin kamfen Atiku Abubakar, Segun Showunmi ya ce da yiwuwar ya sauya sheƙa daga jam'iyyar PDP zuwa APC mai mulki.

Ɗan siyasar ya ce zai bar PDP idan ya fahimci shugabannin jam'iyyar ba su da burin gyarata sai dai ƙara ruguza ta.

Kalaman Segun Showunmi na zuwa ne kwanaki ƙalilan bayan ya gana da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a gidansa da ke jihar Legas.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262