Peter Obi Ya ba da Mamaki, Ya Dauki Alkawari Shiga Dazuka da Afafunsa
- Peter Obi ya sha alwashin shiga dazuzzuka domin ceto wadanda aka sace idan aka zabe shi shugaban kasa a zaben 2027
- Dan takarar shugaban kasa na NDC ya ce gwamnatinsa za ta magance matsalar garkuwa da mutane, tare da tabbatar da tsaron hanyoyin Najeriya
- Obi ya kuma yi alkawarin yaki da cin hanci, samar da ilimi kyauta, da kuma kara samar da wutar lantarki megawatt 10,000
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya dauki gagarumin alkawari game da matsalar garkuwa da mutane.
Peter Obi ya sha alwashin shiga dazuzzuka domin ceto mutanen da aka sace idan aka zabe shi a 2027.

Source: Facebook
Alkawuran da Obi ya dauka
Obi ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga magoya bayansa a wani gangamin yakin neman zabe da aka gudanar a Bayelsa, cewar Punch.
Ya ce gwamnatinsa ba za ta lamunci garkuwa da mutane da rashin tsaro ba, inda ya yi alkawarin samar da yanayin da ‘yan Najeriya za su yi tafiya cikin kwanciyar hankali.
Obi ya ce matakin farko na gwamnatinsa shi ne hada kan ‘yan kasa, tare da tabbatar da cewa babu wani yanki ko rukuni da zai ji an ware shi daga tafiyar Najeriya.
Ya ce:
“Za mu sa Najeriya ta yi aiki yadda ya kamata. Za mu mayar da ita kasa da mutane za su iya rayuwa cikin kwanciyar hankali. Za mu tabbatar da tsaron Najeriya, babu wanda zai zauna a kasar da ba zai iya tafiya a hanya ba.”
Obi ya bukaci a tabbatar da tsaron hanyoyi
Tsohon gwamnan Anambra ya bayyana cewa tafiye-tafiyen da ya yi ta mota a jihohi daban-daban sun nuna bukatar gaggauta inganta tsaron hanyoyin kasar.
Ya ce:
“Na zo Bayelsa da safiyar yau daga Enugu ta mota. Na zagaya sassan Najeriya ta mota. A ranar Talata ina Lokoja, Laraba kuma Akwanga, jiya na kasance a Ebonyi, yau kuma ina Bayelsa. Dole ne a tabbatar da tsaron hanyoyinmu.”
Obi ya kuma soki shugaban kasa Bola Tinubu kan abin da ya bayyana a matsayin gazawarsa wajen ziyartar Bayelsa, duk da gudunmawar da jihar ke bayarwa ga tattalin arzikin Najeriya ta hanyar arzikin man fetur.
Ya tambayi dalilin da ya sa shugaban kasar ke yawan tafiye-tafiye zuwa kasashen waje maimakon mayar da hankali kan ganawa da ‘yan Najeriya a sassa daban-daban na kasar, cewar Vanguard.

Source: Facebook
Zai shiga daji domin ceto al'umma
Dangane da matsalar tsaro, Peter Obi ya yi alkawarin cewa gwamnatin NDC za ta dauki kwararan matakai kan masu garkuwa da mutane, musamman wadanda ke satar dalibai da sauran jama’a.
Ya ce:
“NDC za ta tabbatar da tsaron Najeriya a karkashin gwamnatinta. Idan wani ya sace dalibai ko wani mutum, zan shiga daji. Za mu shiga dajin domin ceto su. Babu wanda zai sake yin irin wannan abu a gwamnatimmu.”
Yadda zai kawo sauki a Najeriya
An ji cewa Pat Utomi ya ce shirin tattalin arzikin NDC ƙarƙashin Peter Obi ya tanadi ƙarfafa Naira zuwa N500 kan dala.
Jam’iyyar ta yi hasashen cewa farashin buhun shinkafa zai sauka daga N55,000 zuwa N27,500, yayin da kwanon garri zai koma N650.
Asali: Legit.ng

