Abba Hikima Ya Fito da Abin da Ya Kamata Mutane Su Sani kan Takarar Pantami da Aminu Gwarzo
- Lauya mai kare hakkin ɗan Adam, Abba Hikima, ya buƙaci INEC ta nemi afuwar Isa Ali Pantami, Aminu Gwarzo da sauran ’yan takarar da ta cire sunayensu
- Ya ce hukumar INEC ta jefa ’yan takarar da magoya bayansu cikin damuwa saboda rashin gudanar da aikinta yadda ya kamata
- Abba ya bukaci INEC ta biya waɗanda abin ya shafa diyya saboda kuɗaɗen da suka kashe wajen shigar da ƙara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Lauya mai kare hakkin ɗan Adam, Abba Hikima, ya ce amincewa da takarar Farfesa Isa Ali Pantami na PDP da Aminu Gwarzo na NDC da INEC ta yi ba abin a yaba ba ne.
Ya buƙaci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta nemi afuwar Pantami, Aminu Gwarzo da sauran ’yan takarar da ta cire sunayensu daga jerin masu neman kujerun zaɓen 2027.

Kara karanta wannan
PRP ta yi kaca kaca da shirin Tinubu, ta taɓo batun kisan Sheikh Yahaya Masussuka

Source: Facebook
Lauyan ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, bayan da INEC ta amince da Pantami a matsayin ɗan takarar gwamnan jihar Gombe na PDP, da kuma Gwarzo a matsayin ɗan takarar gwamnan Kano na NDC.
Ya kuma buƙaci hukumar ta biya waɗanda abin ya shafa diyya, yana mai cewa babu wani abin yabawa a matakin da INEC ta ɗauka na dawo da sunayen ’yan takarar bayan cire su da farko.
Abba Hikima ya soki matakin INEC
A cewarsa, tun farko bai kamata INEC ta cire sunayen ’yan takarar ba, domin hakan ya jefa su da magoya bayansu cikin damuwa ba tare da wani dalili mai ƙarfi ba.
Ya ce abin takaici ne yadda wata hukumar gwamnati mai yawan ma’aikata da kuma kasafin kuɗi mai yawa za ta yi sakaci wajen gudanar da aikinta, sannan daga baya ta dawo da sunayen bayan wasu daga cikin waɗanda abin ya shafa sun garzaya kotu.
Ya bayyana cewa wasu daga cikin ’yan takarar sun kashe kuɗaɗe masu yawa wajen shigar da ƙara, yayin da wasu suka shiga damuwa sosai sakamakon matakin hukumar.
A kalamansa, Abba Hikima ya ce:
“Babu wani abin yabawa domin INEC ta dawo da sunayen Gwarzo, Pantami da sauransu. Tun farko dama bai kamata ta cire ba.
“Haka kawai sai hukumar gwamnati mai kasafin kuɗi da ma’aikata mafi girma ta jefa mutane da mabiyansu cikin zulumi saboda rashin kula da yin aiki yadda ya kamata.
“Sannan daga baya, bayan wasunsu sun shigar da ƙara, sun kashe kuɗaɗe masu yawan gaske, wasu ma jininsu ya hau, kawai sai INEC ta dawo ta ce ta gano suna da gaskiya, kuma sai mutane su riƙa yabon ta? A’a.”

Source: Facebook
Lauyan ya nemi a biya su diyya
Abba Hikima ya jaddada cewa bai kamata INEC ta dawo da sunayen ’yan takarar kawai ba tare da ɗaukar alhakin matsalar da ta jefa su a ciki ba.
Ya ce abin da ya kamata hukumar ta yi shi ne ta nemi afuwarsu tare da biyan su diyya saboda wahala da kuɗaɗen da suka kashe wajen kare haƙƙinsu.
INEC ta amince da korafe-korfe 41
Kun ji cewa hukumar INEC ta amince da ƙorafe-ƙorafe 41 cikin 69 da aka shigar kan jerin sunayen ’yan takarar gwamna na zaɓen 2027, yayin da ta yi watsi da 28.
Hukumar ta ce ƙorafe-ƙorafen sun fito ne daga jam’iyyun siyasa 12 a jihohi 26, inda wasu suka shafi cire sunayen ’yan takara da sauransu.
Asali: Legit.ng

