Shugaba Tinubu Ya Karya Al'adar Ranar Dimokuraɗiyya, Ya Soke Jawabin Kai Tsaye
- Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya soke jawabin kai tsaye ga ƴan kasa wanda aka shirya da misalin ƙarfe 7:00 na safiyar ranar dimokuraɗiyya
- Fadar shugaban ƙasa ta ce Tinubu zai haɗa ya yi jawabi gaba ɗaya a zauren Majalisar Tarayya da misalin karfe 12:00 na rana
- A ranar 12 ga watan Yuni, 2025, Najeriya ke murnar cika shekara 26 cif da dawowar mulkin dimokuraɗiyya ba tare da an samu matsala ba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
State House, Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya karya al’adar gabatar da jawabi ta talabijin kai tsaye ga ‘yan ƙasa domin tunawa da Ranar Dimokuraɗiyya.
A yau Alhamis, 12 ga watan Yuni, Najeriya take bikin ranar dimokuraɗiyya kuma bisa al'ada, shugaba ƙasa kan yi jawabi kai tsaye ga ƴan ƙasa.

Asali: Twitter
Daily Trust ta tattaro cewa a wannan karo, Shugaba Tinubu ya karya wannan al'ada, inda ya soke jawabin kai tsaye da aka shirya da misalin ƙarfe 7:00 na safiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abubuwan da aka tsara a ranar dimokuraɗiyya
Tun farko, kwamitin da ke shirya bikin Ranar Dimokuraɗiyya ya sanar da jerin shirye-shirye don murnar cika shekaru 26 na mulkin dimokuraɗiyya ba tare da katsewa ba a Najeriya.
Daga cikin abubuwan da kwamitin ya shirya akwai:
- Jawabin shugaban ƙasa kai tsaye a ranar 12 ga Yuni, 2025 da ƙarfe 7:00 na safe
- Jawabin shugaban ƙasa ga zaman haɗin gwiwa na Majalisar Dokokin Tarayya da ƙarfe 12:00 na rana
- Lakca ta musamman kan Ranar Dimokuraɗiyya a Ɗakin Taro na Fadar Shugaban Ƙasa da ƙarfe 4:00 na yamma
Shugaba Tinubu ya soke jawabi ga ƴan ƙasa
Sai dai a cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, Segun Imohiosen, ya fitar a daren Laraba, ya bayyana cewa an sauya jadawalin abubuwan da Tinubu zai yi a wannan rana.
Imohiosen ya ce, tun da shugaban ƙasa zai gabatar da jawabinsa a gaban zaman haɗin gwiwa na Majalisar Tarayya, babu buƙatar sai ya yi jawabi kai tsaye ga ƴan ƙasa.

Asali: Twitter
Bola Tinubu zai yi jawabi a Majalisar Tarayya
A cewarsa, Mai girma shugaban ƙasa zai haɗa duk wani saƙo da yake son isarwa ga ƴan ƙasa a cikin jawabin da zai yi a zauren Majalisar Tarayya da ke Abuja, rahoton Leadership.
“Tun da shugaban ƙasa Bola Tinubu zai halarci zaman haɗin gwiwa na Majalisar Tarayya, an soke gabatar da jawabinsa na talabijin da aka shirya a ranar 12 ga Yuni.
"Shugaban ƙasa zai gabatar da jawabin na sa kai tsaye ga ƴan kasa daga zauren majalisar tarayya,” in ji Imohiosen.
Bola Tinubu ya yi wa Wike tayin shiga APC
A wani labarin, kun ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya fara zawarcin ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike.
Shugaba Tinubu ya yi wa Wike tayin shiga APC a wurin kaddamar da sababbin tituna da ministan ya jagoranci aiwatarwa a babban birnin tarayya.
Ya ce ƙofar APC a buɗe take kuma za ta karɓi tsohon gwamnan hannu bibbiyu idan ya yanke shawarar sauya sheƙa daga PDP.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng