Majalisar Tarayya Ta Kafa Doka, Ta Canza Tsarin Jawabin Ranar Dimokuraɗiyya a gaban Tinubu
- Majalisa ta amince ranar 12 ga watan Yuni ta zama ranar da shugaban ƙasa zai riƙa yin jawabin ranar dimokuraɗiyya a gabanta kowace shekara
- Wannan mataki dai zai ba shugaban ƙasa damar gabatar da jawabin ranar dimokuraɗiyya na kowace shekara a zaman haɗin guiwa na majalisar tarayya
- Kakakin Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas ne ya gabatar da kudirin a gaban shugaba Tinubu kuma galibin ƴan Majalisa suka goyi baya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Majalisar Tarayya ta amince da ranar 12 ga Yuni a matsayin ranar da shugaban ƙasa zai rika gabatar da jawabi a gabanta kowace shekara.
Hakan na nufin shugaban ƙasa zai riƙa bayyana a zaman haɗin gwiwa na Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai domin yin jawabin ranar dimokuraɗiyya a kowace ranar 12 ga Yuni.

Asali: Facebook
Channels tv ta tattaro cewa an yanke wannan shawara ne a ranar Alhamis yayin zaman haɗin guiwa wanda shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da jawabi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda Majalisa Tarayya ta yi sabuwar doka
Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ne ya jagoranci zaman, kuma ya sanar da amince wa da wannan mataki.
Shugaban Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas, ne ya gabatar da kudirin cewa a dinga yin jawabin ne a kowace ranar 12 ga Yuni 2025.
Da yake bayani ga Shugaba Tinubu, Sanata Akpabio ya ce:
“Ranka ya daɗe a cikin kyakkyawan jawabin da Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, ya gabatar, ya buƙaci a ƙarfafa ranar 12 ga Yuni a matsayin ranar da shugaban ƙasa zai rika yin jawabi ga Majalisar Tarayya."
"Zan sanya wannan kudiri a gabanmu domin kaɗa kuri'a, masu goyon baya su ce 'Aye' waɗanda ba su yarda ba su ce 'Nay', masu goyon baya ne suka fi rinjaye."
Daga nan shugaban Majalisar Dattawa ya juya ga Shugaba Tinubu yana cewa:
“Shugaban Ƙasa, wannan mataki na majalisar ƙasa ne, kuma an yanke shi a gabanka.”
Majalisar Dattawa ta fara kawo kudirin
Tun a ranar 10 ga Yuni, Majalisar Dattawa ta fara nuna aniyarta na saka jawabin shugaban ƙasa na ranar 12 ga Yuni cikin tsarin doka domin girmama ranar a tarihin dimokuraɗiyyar Najeriya.
Shugaban masu rinjaye, Sanata Opeyemi Bamidele, ya ce sun fara aikin samar da dokar da za ta tabbatar da jawabin shugaban ƙasa na ranar 12 ga Yuni a kowace shekara.

Asali: Twitter
“Muna fatan gabatar da kudirin doka nan ba da jimawa ba domin a tabbatar da ranar 12 ga Yuni a matsayin lokacin da shugaban ƙasa zai rika yi wa ƙasa jawabi ta hannun Majalisar Tarayya.
"Wannan rana ce ta tarihi wacce ta fi dacewa da irin wannan jawabi,” in ji Sanata Bamidele.
A halin yanzu kudirin ya zama doka bayan ƴan Majalisar sun amince da shi a zaman haɗin guiwa na ranar dimokuraɗiyya ta bana 2025.
Bola Tinubu ya tuna Muhammadu Buhari
A wani labarin, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yabi Muhammadu Buhari bisa ayyana ranar 12 ga Yuni a matsayin ranar dimokuraɗiyya.
Shugaba Tinubu ya ce wannan abin alheri da tsohon shugaban kasa Buhari ya yi, ya gyara zaluncin da aka yi a baya.
Ya kuma jaddada cewa matakin da Buhari ya ɗauka ya nuna Cif M.K.O. Abiola da abokin takararsa Babagana Kingibe a matsayin waɗanda suka lashe zaɓen shugaban ƙasa na 12 ga Yuni, 1993.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng