Hukumar Kwastam Ta Rusa Tarihin da Ta Kafa na Samun Kudi Mafi Yawa a Rana Guda

Hukumar Kwastam Ta Rusa Tarihin da Ta Kafa na Samun Kudi Mafi Yawa a Rana Guda

  • A filin jirgin Murtala Muhammad, kwastam ta karya tarihin kuɗin shiga mafi yawa da aka taba samu a rana
  • Sabon shugaban reshen ya sha alwashin bin tafarkin magabancinsa da ya tatso sama da N6bn a rana guda
  • Hukumar ta tara sama da Naira biliyan 175.6 daga Janairu zuwa Oktoba 2026, tare da ƙwace ƙwayoyi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Lagos - Hukumar Kwastam ta Najeriya reshen filin jirgin saman Murtala Muhammed (MMAC) a Legas ta yi abin yabo.

Kwastam ta karya tarihin kuɗin shiga na rana da ta tara Naira biliyan 6.2 a awanni 24, a baya ba a taba zarce N1.64bn ba.

Kwastam
Jami'an Kwastam na Filin jirgin Murtala Muhammad a Legas Hoto: Nigeria Customs Service
Source: Facebook

Daga N1bn an samu N6bn a rana

Hukumar ta sanar da duniya wannan a wani bayani da aka yi a shafinta na Facebook ranar Alhamis.

Idan aka kwatanta da tsohon tarihin da jami’an suka ajiye, kuɗin shigan da kwastam ta samo a ranar ya karu da 533% kenan.

Kara karanta wannan

Matasa sun shiga babbar matsala da suka jefi magoya bayan APC a tawagar gwamna

Babban jami’in Kwastam mai barin gado a reshen, ACG Godwin Otunla ya bayyana hakan ranar Talata, 27 ga Oktoba, 2026.

Jami’in ya yi bayanin nasarar ne yayin bikin miƙa ragamar shugabancin kwastam na filin jirgin ga ACG Mahmood Mundi.

Kwastam sun samu N175bn a watanni 10

Da yake bayyana nasarorin da aka samu cikin shekarar, Otunla ya ce jami’ansa sun samu nasara sosai wajen tattara kuɗin shiga.

Ya ce an karfafa hulɗa da masu ruwa da tsaki, tare da tabbatar da zaman lafiya a wurin aiki.

A filin jirgin, ACG Godwin Otunla ya ce sun tara N175,680,895,471.74 daga watan Janairu zuwa watan nan na Oktoba 2026.

Babban jami’in ya ce hukumar kwastam ta miƙa biliyoyin kuɗi zuwa cikin asusun Gwamnatin tarayya.

Ya ce:

“Reshen ya tsara matakan inganta tattara kuɗin shiga ta hanyar toshe hanyoyin da ake bi wajen kauce wa biyan haraji, amfani da na’urorin tantance kaya, gudanar da cikakken binciken kaya, da kuma aiwatar da tsarin tantance haɗari bisa bayanan sirri.”

Kara karanta wannan

Rana ba ta karya: Yau INEC za ta yi matsaya kan Pantami da wasu 'yan takara

Hukumar kwastam ta karbe kwayoyi a filin jirgi

Otunla ya bayyana cewa yaƙi da fasa ƙwauri ya haifar da ƙwace fakiti 178 na maganin Tramadol da kwalaye 50 na tabar wiwi.

Ya ce jimillar kuɗin harajin kayan da aka ƙwace ya kai N118,228,874,754.28, kuma an miƙa su ga wakilin Hukumar NDLEA.

Da yake yaba wa nasarorin magabacinsa, sabon shugaban ya ce zai yi aiki bisa ka’ida da gaskiya domin inganta ayyukan hukumar.

Ya ce:

“Ina ganin hulɗa da masu ruwa da tsaki muhimmin ginshiƙi ne na samun nasara."

Mundi ya ce haɗin kan wakilai da sauran abokan hulda da bin ƙa’idoji na da matuƙar muhimmanci wajen cinma muradu.

Ranar da aka samu N28bn a gidan kwastam

An ji lokacin da Hukumar Kwastam ta reshen Apapa a Legas ta kafa tarihi ta hanyar tatro kudin shiga na N28.1bn a rana guda.

Shugaban reshen, Emmanuel Oshoba, ya bayyana cewa kudin za su taimaka wajen gina ababen more rayuwa a kasar.

Wannan nasarar ta zo ne biyo bayan kokari da dabarun da shugaban kwastam na kasa, Bashir Adeniyi, ya kawo da ya shiga ofis.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng