Babban Malami Ya Hango Matsala, Ya ba Tinubu Mafita kan Cire Shettima a Zaɓen 2027
- Fitaccen malamin cocin nan, Primate Ayodele ya buƙaci Shugaba Bola Tinubu ya jure wa duk wata matsin lamba, ka da ya canza Shettima a 2027
- Ayodele ya yi hasashen cewa nan gaba za a haɗa Tinubu da Shettima faɗa amma ka da hakan ya sa shugaban kasa ya sauya abokin takara
- Malamin ya ce tazarcen shugaba Tinubu zai raba kawunan Arewa, yana mai cewa akwai bukatar Tinubu ya shirya fuskantar yaƙi mai tsanani
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Jagoran cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Primate Elijah Ayodele, ya shawarci Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da kada ya sauya mataimakinsa a zaɓen 2027.
Fitaccen malamin, wanda ya shahara wajen hasashen abubuwan da za su faru, ya ce bai kamata Tinubu ya canza Kashim Shettima, a matsayin abokin takararsa a 2027 ba.

Asali: Twitter
Tribune Nigeria ta rahoto cewa Ayodele ya bayyana haka ne a wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Osho Oluwatosin, ya sanya wa hannu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
2027: Malami ya bukaci Tinubu ya tafi da Shettima
Primate Ayodele ya bukaci shugaban ƙasa da ya shanye duk wata matsin lamba na sauya Shettima, amma ya gargade shi da ya shirya tsaf domin fuskantar rigima mai zafi a tsakaninsu.
Malamin addinin ya ce tazarce da Tinubu ke shirin nema zai haddasa rabuwar kai a Arewacin Najeriya tare da janyo rudani da rikice-rikice.
Don haka idan har yana son ya guje wa abin da za a zarge shi da shi, Ayodele ya ce dole Shettima ya ci gaba da kasancewa tare da shi a matsayin abokin takara.
'Sauya Shettima zai jawo wa Tinubu matsala'
Ya ce:
“Neman tazarce da Tinubu zai yi a 2027 zai raba kan Arewa. Zai haifar da rarrabuwar kawuna da rikice-rikice masu yawa. Ka da shugaban ƙasa ya kuskura ya sauya Shettima.
“Sai dai dole ne ya shirya fuskantar gwabzawa mai tsanani. Za su samu matsaloli irin na zamanin Obasanjo da Atiku. Amma kada ya cire Shettima, domin hakan ne zai ba shi damar tsira a 2027.”

Asali: Facebook
Rikici zai shiga tsakanin Tinubu da Shettima?
Primate Ayodele ya ƙara da cewa rikicin da zai faru zai sanya Shettima ya rasa tasiri a ofishinsa kuma za a hana shi kataɓus a matsayinsa na mataimakin shugaban ƙasa.
"Wannan rikicin zai iya sanya Mataimakin Shugaban Ƙasa ya kaurace wa ofishinsa. Zai rage tasirinsa kwarai da gaske, saboda matsin lamba zai yi yawa.”
Haka kuma, malamin ya ja kunnen Tinubu da ya yi hattara da sababbin ’yan siyasar da ke shigowa APC daga jam’iyyun adawa, domin wasu daga cikinsu ba za su ƙara masa ƙarfi ba sai dai su rage masa.
Peter Obi ya sake sukar gwamnatin Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa Peter Obi ya sake nuna ɓacin ransa kan yadda abubuwa ke ƙara taɓarɓarewa a Najeriya karkashin gwamnatin APC.
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa ya buƙaci ƴan Najeriya su yi duk mai yiwuwa wajen ganin APC ba ta yi tazarce kan madafun iko a 2027 ba.
A cewarsa, shekaru biyu da kafa gwamnati, har yau Najeriya na fama da kashe-kashe, yunwa, hauhawar farashi, talauci, faɗuwar darajar Naira da rashin aikin yi.
Asali: Legit.ng