Jigon APC Ya Yi wa Atiku Tatas, Ya Bukaci Ya Yi Ritaya daga Siyasa
- Alwan Hassan ya bukaci Atiku Abubakar ya yi ritaya daga siyasa maimakon sake neman shugabancin Najeriya a zaɓen 2027
- Jigon na APC ya zargi Atiku da kasa samar da ci gaba mai ma’ana a Arewacin Najeriya duk da shekarun da ya yi a manyan muƙaman gwamnati
- Alwan Hassan ya kare gwamnatin Tinubu, yana mai cewa ci gaban tattalin arziki, ilimi da manyan ayyukan more rayuwa sun cancanci a sake ba shugaban ƙasar wa’adi na biyu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Wani jigon jam’iyyar APC, wanda kuma yana cikin masu magana da yawun Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na jam’iyyar, Mallam Alwan Hassan, ya yi kakkausar suka kan tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar.
Alwan Hassan ya bukaci Atiku ya janye daga takarar shugaban ƙasa ta 2027, yana mai cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasar ba shi da wani sabon abu da zai iya yi wa ’yan Najeriya, musamman mazauna Arewa.

Source: Facebook
Jigon na APC ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da aka gudanar a Kano ranar Alhamis, 29 ga watan Oktoban 2026, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
Me Alwan Hassan ya ce kan Atiku Abubakar?
Alwan Hassan ya zargi Atiku da kasa magance manyan matsalolin ci gaban Arewacin Najeriya, duk da shekarun da ya shafe yana riƙe da manyan muƙaman gwamnati da kuma ƙoƙarin da ya sha yi na zama shugaban ƙasa.
Ya ce ya kamata tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya hakura da neman shugabanci, ya koma jin daɗin rayuwa bayan shekarun da ya yi a harkokin gwamnati.
A kalamansa:
“Atiku ya kamata ya yi ritaya ya more duk abin da ya rage masa daga arzikin da ya samu a zamanin aikinsa a hukumar kwastam. Atiku, ka je ka yi ritaya! Ba ka da abin da za ka iya bayarwa.”
Alwan Hassan ya kuma tambayi irin gudunmawar da Atiku ya bayar wajen ci gaban Arewa, yana mai cewa bai nuna isasshen jajircewa wajen inganta yankin ba duk da yadda yake ikirarin kare muradunsa.
Ya kare gwamnatin Bola Tinubu
A gefe guda, Alwan Hassan ya bayyana goyon bayansa ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa sauye-sauyen tattalin arziki da zuba jari a manyan ayyukan more rayuwa, ilimi da walwalar jama’a sun cancanci a sake ba shugaban ƙasar wa’adi.
Ya yi nuni da alkaluman da ya ce sun nuna tattalin arzikin Najeriya ya bunƙasa da kashi 4.43 cikin 100 a zangon biyu na shekarar 2026, idan aka kwatanta da kashi 2.74 cikin 100 a shekarar 2023.
Haka kuma, ya ambaci cewa ajiyar kuɗaɗen waje ta Najeriya ta ƙaru zuwa dala biliyan 55.1 a ranar 9 ga Oktoban 2026.
Alwan Hassan ya amince cewa cire tallafin man fetur da sauye-sauyen tsarin canjin kuɗaɗen waje sun jefa ’yan Najeriya cikin tsadar rayuwa da matsin tattalin arziki.
Sai dai ya ce matakan na taimakawa wajen magance matsalolin tattalin arzikin da suka daɗe suna addabar ƙasar.

Source: Twitter
Nyesom Wike ya ragargaji Atiku Abubakar
A wani labarin kuma, kun ji cewa Nyesom Wike, ya kalubalanci tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, da ya bayyana irin nasarorin da ya samu a shekaru takwas da ya yi a kan mulki.
Wike ya kuma buƙaci ’yan Najeriya su yi la’akari da sukar da tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya yi wa tsohon mataimakinsa, yayin da ake tunkarar zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Asali: Legit.ng


