Nasara daga Allah: Dakarun Sojojin Najeriya Sun Tura Yan Ta'adda Sama da 200 Lahira
- Dakarun sojojin Najeriya sun kashe ’yan ta’adda 217 tare da kama mutum 333 da ake zargi da ta’addanci a watan Oktoba 2026
- Sojojin sun kuɓutar da mutane 349 da aka yi garkuwa da su, yayin da ’yan ta’adda 70 suka miƙa wuya
- Rundunar sojin ta kuma ƙwato makamai 105 da harsasai 3,174, tare da kuɓutar da kuɗin fansa da ake zargin ya kai Naira miliyan 17 a Kano da Borno
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Dakarun rundunar sojojin Najeriya sun kashe ’yan ta’adda 217 tare da kama mutum 333 da ake zargi da ta’addanci a sassan Najeriya.
Dakarun sojin sun kuma kuɓutar da mutane 349 da aka yi garkuwa da su a sassa daban-daban na ƙasar nan a watan Oktoba na shekarar 2026.

Source: Facebook
Leadership ta ruwaito cewa Babbar Hedikwatar Tsaro ta Ƙasa (DHQ) ce ta bayyana hakan, inda ta ƙara da cewa ’yan ta’adda 70 sun miƙa wuya ga sojoji a cikin wannan lokaci.
Daraktan yaɗa labarai na ayyukan tsaro na rundunar, Manjo Janar Michael Onoja, ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai ranar Juma’a. Ya ce sojojin sun kuma ƙwato makamai 105 da harsasai 3,174.
Haka kuma, ayyukan yaƙi da satar ɗanyen mai sun taimaka wajen ƙwato lita 756,837 na kayayyakin ɗanyen mai da aka sace, tare da lalata wuraren tace mai ba bisa ƙa’ida ba guda 49.
An kai hare-hare 98 a wata
Kakakin rundunar tsaron ya ce rundunar sojojin ta fuskanci hare-hare 98 a wuraren da take gudanar da ayyukan yaƙi daban-daban tsakanin 30 ga Satumba zuwa 30 ga Oktoba.
Sai dai ya ce dakarun sun mayar da martani mai ƙarfi kan hare-haren, inda suka yi artabu da maharan tare da amfani da ƙarfin makamai mafi girma wajen fatattakarsu.
Babban hafsan tsaron, Janar Olufemi Olatubosun Oluyede ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa ba za a bar wani yunƙuri ba wajen kamo waɗanda suka aikata laifukan tare da hukunta su.
An gargaɗi sojoji kan sakaci
Babban hafsan tsaron ya yaba da jajircewar sojoji a dukkan wuraren da suke gudanar da ayyukan tsaroz inda ya buƙace su da su ci gaba da kasancewa masu ladabi, bin ƙa’idojin amfani da makamai da kuma mutunta haƙƙin bil’adama.
Ya kuma gargaɗe su da su guji yin sakaci, musamman yayin da ake tunkarar lokacin bukukuwan ƙarshen shekara.
Janar Oluyede ya buƙaci sarakunan gargajiya, shugabannin al’umma, matasa da sauran masu ruwa da tsaki da su riƙa kai rahoton duk wata barazana cikin gaggawa, su guji ɗaukar doka a hannu tare da hana masu laifi samun mafaka.

Source: Twitter
Ya kuma yi kira ga kafafen yaɗa labarai da su tabbatar da sahihancin rahotanninsu, musamman kan batutuwan da suka shafi rikice-rikicen al’umma, domin kada wani rahoto ya haddasa tashin hankali ko ya kawo cikas ga ayyukan sojojin da ake gudanarwa.
Ya yi gargaɗin cewa babu wani ɗan ta’adda ko mai taimaka musu da zai tsira daga hukunci da zarar an kama shi.
Sojoji sun yi raga-raga da yan ISWAP
Kun ji cewa rundunar sojojin saman Najeriya ta kashe ’yan ta’addar ISWAP 15 a wani samame da ta kai kusa da Kerenoa, a Ƙaramar Hukumar Marte ta Jihar Borno.
Sojojin sun kuma lalata wani wurin da ake zargin ’yan ta’addar ke amfani da shi wajen adana kayan ƙera bama-bamai.
Asali: Legit.ng


