Najeriya Ta Yi Babban Rashi, Tsohuwar Ambasada a Ƙasashe 2 Ta Riga Mu Gidan Gaskiya
- Tsohuwar ambasadar Najeriya a Zambia da Malawi, Ibironke Adefope ta mutu tana da shekaru 73 a duniya
- Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya tabbatar da rasuwar, inda ya miƙa sakon ta'aziyya ga iyalai da ƴan uwan Adefope
- Makinde ya bayyana marigayiyar a matsayin gwarzuwar mace, wacce ta ba da gudummuwa wajen ci gaban Oyo da Najeriya baki ɗaya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Oyo - Tsohuwar jakadar Najeriya a ƙasashen Zambia da Malawi, kuma mamba mai daraja a Majalisar Dattawan Jihar Oyo, Ambasada Ibironke Adefope, ta rasu.
Rahotanni sun nuna cewa tsohuwar ambasadar ta mutu yau Laraba, 11 ga watan Yuni, 2025 tana da shekaru 73 a duniya.

Asali: Facebook
Leadership ta tattaro cewa an haifi Ambasada Adefope a ranar 23 ga Fabrairu, 1952, a birnin Ibadan na jihar Oyo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Marigayiyar ta samu nasarori masu ɗumbin yawa a rayuwarta kama daga fagen ilimi, aikin diflomasiyya da kuma ci gaban al’umma.
Gwamma Makinde ya tabbatar da rasuwar
Gwamnan Jihar Oyo, Injiniya Seyi Makinde, ya bayyana alhininsa game da rasuwar Adefope, yana cewa ta kasance “gwarzuwar mace” kuma “ta shiga tarihin da ba za a manta da ita ba.”
Gwamnan ya ce:
“Labarin rasuwar Mama Ibironke Adefope, tsohuwar Jakadiyar Najeriya a Zambia kuma mamba a Majalisar Dattawan Jihar Oyo, ya girgiza ni matuƙa.”
“Sai dai, dole ne mu miƙa wuya ga kudirar Allah wanda ke bayarwa kuma yake ɗauke wa a lokacin da ya so.”
Gudummuwar da tsohuwar ambasadar ta bayar
Makinde ya yabawa Marigayiya Adefope kan yadda ta sadaukar da rayuwarta wajen yiwa ƙasa hidima da jiharta, kamar yadda Punch ta rahoto.
Ya kuma bayyana cewa ta fito daga sanannen gida watau gidan Eegunjenmi na Itutaba, Oje a Ibadan, kuma jika ce ga fitaccen ɗan siyasa, Cif Meredith Adisa Akinloye.
“Mama ta kasance jarumar mace, wadda ta bayar da gagarumar gudunmawa wajen ci gaban Jihar Oyo da Najeriya gaba ɗaya. Ta bar baya mai kyau wanda ta gada daga iyayenta.

Asali: Twitter
Seyi Makinde ya ƙara da cewa za a yi matuƙar rashinta, musamman goyon baya da hawarwarin da take yawan bayar wa a Oyo.
“Allah ya ba iyalanta da dukan waɗanda ta bari baya haƙuri da juriyar rashinta," in ji shi.
Tarihin karatun Ibironke Adefope
Adefope ta fara karatunta a makarantar St. Anne’s, Molete, Ibadan, sannan ta tafi makarantar International School, Jami’ar Ibadan (ISI), kafin ta tafi Amurka inda ta samu digiri na farko da na biyu.
Daga bisani, Jami’ar Fasaha ta Ladoke Akintola (LAUTECH), Ogbomoso ta ba ta digirin girmamawa na Dakta.
Babban sakatare a Taraba ya rasu a asibiti
A baya mun kawo maku labari cewa babban sakatare a ofishin hulɗa da Abuja na gwamnatin Jihar Taraba, Dauda Maikomo ya riga mu gidan gaskiya.
Gwamnatin Taraba karkashin jagorancin Gwamna Agbu Kefas ta tabbatar da rasuwar Maikomo a wata sanarwa da ta fitar a safiyar yau Laraba.
Ta bayyana mamacin a matsayin jajirtaccen jami’in gwamnati wanda ya bayar da gudunmuwa sosai ga ci gaban Jihar Taraba da ƙasar nan baki ɗaya.
Asali: Legit.ng