Kuɗin Yawon Sallah Sun Jawo Matsala, Uwa Ta Kashe Ɗiyarta kan N100 a Zariya

Kuɗin Yawon Sallah Sun Jawo Matsala, Uwa Ta Kashe Ɗiyarta kan N100 a Zariya

  • Ana zargin wata matar aure mai suna Khadija da lakaɗawa ɗiyarta Fadila dukan kawo wuƙa har yarinyar ƴar shekara 11 ta mutu
  • Shaidu sun bayyana matar ta zargi Fadila da satar mata N100 da aka ba ta lokacin bukukuwan babbar Sallah a Zariya a jihar Kaduna
  • Rahoto ya nuna cewa ƴan sinitiri suka fara shiga lamarin, amma tuni suka miƙa matar ga ƴan sanda domin gudanar da bincike

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Zaria, Kaduna - Wata mata da aka bayyana sunanta da Khadija a taƙaice na fuskantar zargi na dukan ‘yarta mai suna Fadila, mai shekaru 11, har ta mutu a Zariya, Jihar Kaduna.

Ana zargin Khadija da halaka ɗiyarta ne saboda ta sace mata ₦100 da aka ba ta a lokacin bukukuwan babbar Sallah.

Kudin yawon sallah sun hada faɗa a Zaria.
Ana zargin wata matar aure ta kashe ɗiyarta kan N100 a Zaria Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar Leadership ta rahoto cewa matar auren ta hau ɗiyarta da duka ne bayan ɓatan N100, lamarin da ya yi ajalin yarinyar ƴar shekara 11 kacal.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda mahaifiya ta kashe ƴarta kan N100

Shaidu sun bayyana cewa Khadija ta zargi Fadila da satar kuɗin, kuma cikin fushi, ta dauki wani abu ta fara dukan yarinyar, wanda hakan ya yi sanadin mutuwarta.

Wasu mazauna yankin da lamarin ya auku sun ce ba wannan ne karo na farko da Khadija ke dukan Fadila ba, musamman kan abin da ya shafi kudi.

A cewar mutane, suna zargin matar tana yawan gallaza wa Fadila musamman game da batutuwa suka shafi tallan kayan da Fadila ke yi mata a bakin titi.

Wane mataki mahaifin Fadila ya ɗauka?

Mahaifin yarinyar, Malam Mustapha Musa, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai, ya ce abin ya faru lokacin yana wurin aiki, in ji rahoton Daily Post.

Malam Mustapha ya shaidawa manema labarai cewa yana wurin aiki lokacin da lamarin ya faru, bayan ya dawo gida ne aka sanar da shi rasuwar ‘yarsa.

Magidancin ya ce tuni ya dauki gawarta zuwa garinsu da ke jihar Kano domin yi mata jana’iza kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

Na kai matar wurin yan sanda.
Yan sanda sun fara bincike kan kisan Fadila a Zaria Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Ƴan sanda za su gudanar da bincike

Khadija ta amsa cewa lallai ta bugi Fadila, amma ba da niyyar kashe ta ba, inda ta danganta abin da ta aikata da “matsanancin damuwa da fusatar da ta yi a lokacin.”

Wasu ‘yan sintiri na unguwar ne suka fara shiga tsakani kafin daga bisani su mika lamarin ga ‘yan sanda don ci gaba da bincike.

A halin yanzu, matar da ta aikata wannan ɗanyen aiki na hannun ƴan sanda kuma ana sa ran za su gurfanar da ita a gaban kotu da zaran an kammala bincike.

Ango ya daɓa wa amarya wuƙa har lahira

A wani labarin, kun ji cewa wani sabon ango ya yi ajalin amaryarsa da wuƙa a yankim ƙaramar hukumar Gwarzo ta jihar Kano.

Rahotanni sun tabbatar da cewa matashin da ake zargi ya kashe sabuwar amaryarsa ta hanyar yanka ta da wuka wanda ya yi sanadin rasa ranta.

An ce abin ya faru da rana tsaka bayan sallar Azahar, inda aka samu mamaciyar da munanan raunuka a wuyanta da cinyarta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262