Sojoji Sun Ragargaji 'Yan Ta'adda a Borno, Sun Kashe kusan 50

Sojoji Sun Ragargaji 'Yan Ta'adda a Borno, Sun Kashe kusan 50

  • Dakarun Operation Hadin Kai sun kashe ’yan ta’adda 44 da ake zargin ’yan Boko Haram da ISWAP ne a wasu hare-hare da suka kai a jihar Borno
  • Dakarun sun kuma raunata wasu da dama, tare da lalata motocinsu, babura da kayayyakin ƙera bama-bamai a dazukan
  • Rundunar sojin ta ce hare-haren sun faru ne a Kukawa da yankin Tafkin Chadi, inda ta jaddada aniyar ci gaba da matsa lamba kan ’yan ta’adda a Arewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Maiduguri – Dakarun haɗin gwiwa na Operation Hadin Kai sun kashe ’yan ta’adda 44 da ake zargin ’yan Boko Haram da ƙungiyar ISWAP ne a wasu hare-haren soji da suka kai a sassa daban-daban na jihar Borno.

Hare-haren sun kuma yi sanadin jikkatar wasu da dama daga cikin ’yan ta’addan, yayin da sojojin suka lalata motocinsu, babura da kayayyakin da ake amfani da su wajen ƙera bama-bamai.

Kara karanta wannan

Sojoji sun yi ruwan wuta kan 'yan ISWAP, an kashe manyan kwamandoji da mayaka

Sojojin Najeriya a daji
Dakarun NAjeriya a fagen daga. Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Getty Images

Punch ta wallafa cewa kakakin watsa labarai na rundunar Operation Hadin Kai ta Arewa maso Gabas, Kyaftin Mohammed Goni, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a safiyar Alhamis.

An kashe ’yan ta’adda 28 a Kukawa

Goni ya ce dakarun Operation Hadin Kai sun ci gaba da kai hare-hare kan ’yan ta’adda bisa bayanan sirri da binciken da aka gudanar a wurare daban-daban na yankin ayyukansu.

Ya bayyana cewa a ranar 26 ga Oktoba, 2026, sojoji sun fafata da wasu da ake zargin ’yan ta’adda ne a wurare daban-daban na ƙaramar hukumar Kukawa ta jihar Borno.

A cewarsa, bayan tantance illar hare-haren, an tabbatar da kashe ’yan ta’adda 28, yayin da wasu shida suka samu raunuka.

An kashe wasu 8 a Tafkin Chadi

Kakakin rundunar ya ce a ranar 28 ga Oktoba, 2026, rundunar sojojin ruwan Najeriya da ke sansanin tafkin, wadda ke aiki daga Baga, ta kai hare-hare kan wasu wuraren da ake zargin ’yan ta’adda ne ke amfani da su a yankin Tafkin Chadi.

Kara karanta wannan

Rana ba ta karya: Yau INEC za ta yi matsaya kan Pantami da wasu 'yan takara

The nation ta rahoto ya ce binciken farko ya nuna cewa an kashe ’yan ta’adda takwas, yayin da wasu 10 suka samu raunuka daban-daban.

Goni ya ƙara da cewa wani harin sama na daban ya tarwatsa wani yunƙuri na ’yan ta’adda na dasa bama-bamai a kan hanyoyi.

Taswirar jihar Borno
Taswirar jihar Borno a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

A yayin wannan hari, an kashe mutum takwas da ake zargin suna cikin tawagar, sannan aka lalata motarsu, babura da kayayyakin ƙera bama-bamai.

Goni ya bayyana cewa nasarorin da aka samu sun nuna yadda hare-haren haɗin gwiwa da ake gudanarwa bisa bayanan sirri ke ci gaba da matsa wa ƙungiyoyin ’yan ta’adda lamba.

An sace mai juna biyu a Kaduna

A wani labarin, kun ji cewa wata mata mai juna biyu mai suna Jamila da ’yan bindiga suka sace daga gidanta da ke Alrahus Estate, Millennium City, a jihar Kaduna, ta shafe mako uku a daji.

An sace Jamila ne a ranar 6 ga Oktoba tare da Abubakar Zakka, matarsa da ’yarsu mai watanni shida, lokacin da ’yan bindigar suka kai farmaki gidansu da ke ƙaramar hukumar Chikun.

Wata majiya da ke da masaniya kan tattaunawar neman sakin mutanen ta shaida cewa masu garkuwa da mutanen sun kira a ranar Talata, suka miƙa wayar ga Jamila, inda ta ce cikin ta ya zube.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng