'Mun cika alƙawura': Radda Ya Nemi Katsinawa Su Sake ba Shi Dama a 2027
- Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, na ci gaba da ziyarar yankunan jihar Katsina yayin da yake yakin neman zabe
- Ziyarar ta sa ta kai shi karamar hukumar Dandume inda ya gana da masu ruwa da tsaki da magajin Dandume
- A yayin ziyarar, Katukan Katsina kuma Hakimin Dandume, ya yaba wa Gwamna Radda kan alkawuran da ya cika
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Katsina - Katukan Katsina kuma Hakimin Dandume, Alhaji Jafar Ibrahim, wanda ya samu wakilcin Magajin Garin Dandume, ya yaba wa Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda.
Alhaji Jafar Ibrahim ya yaba wa Gwamna Radda ne bisa cika alkawuran da ya ɗauka wa al’ummar Ƙaramar Hukumar Dandume a lokacin yaƙin neman zaɓen shekarar 2023.

Source: Facebook
Mai taimakawa Gwamna Radda kan harkokin kafafen yada labarai, Mustapha Samaila Ingawa, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a shafinsa na Facebook ranar Juma'a, 30 ga watan Oktoban 2027.
Gwamna Radda ya samu yabo
A cikin sanarwar ya ce Hakimin ya bayyana hakan ne a lokacin da Gwamna Radda ya kai masa ziyarar ban-girma a fadarsa, a rana ta uku ta gangamin yakin Neman Zaɓen Tinubu/Dikko 2027 da ake gudanarwa a faɗin jihar inda ya gana da sarakunan gargajiya da masu ruwa da tsaki na Karamar Hukumar Dandume.
“Na karɓe ku a nan a lokacin yaƙin neman zaɓen shekarar 2023, kuma zan iya tabbatar muku da cewa kun cika dukkan alkawuran da kuka ɗauka wa mutunenmu,” in ji Magajin Dandume.
Ya bayyana jin daɗinsa musamman kan ɗaga matsayin Babban Cibiyar Kiwon Lafiya ta Dandume (CHC) zuwa Babban Asibiti, samar da kayan aikin noma, gyare-gyaren da aka yi wa sarakunan gargajiya da malaman addini, shirye-shiryen bayar da tallafin karatu, Shirin Bunƙasa Al’umma (CDP), da sauran ayyukan raya fannonin ilimi, tsaro, noma da kiwon lafiya.
Gwamna Radda ya yi jawabi
A nasa jawabin, Gwamna Radda ya bayyana cewa ziyartar sarakunan gargajiya al’ada ce da tawagar yaƙin neman zaɓen ke bi a dukkan wuraren da ta ziyarta.

Kara karanta wannan
Isa Ashiru ya fito da gaskiyar zance bisa zargin ya fallasa El Rufai kan rashin tsaro a Kaduna
Ya kuma yi tsokaci kan sauye-sauye da gwamnatinsa ta kawo a hukumomin sarakunan gargajiya da na addini, shirye-shiryen bunƙasa al’umma da kuma tallafin da ake bai wa harkar noma, musamman noman rani.
Gwamnan ya sake jaddada cewa ɗaga matsayin Babban Cibiyar Kiwon Lafiya ta Dandume zuwa Babban Asibiti na daga cikin ƙudurin gwamnatinsa na cika alkawuran da ta ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓen 2023.
Haka kuma, Gwamna Radda ya sanar da amincewa da shirin zamanantar da Kasuwar Dandume.
Radda ya ce an samu ci gaba a fannin tsaro
Gwamnan ya yi tsokaci kan ci gaban da aka samu a fannin tsaro, tare da bayyana muhimmancinsa wajen bunƙasa harkokin noma da ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’umma a yankin.
Ya kuma bayyana shirye-shiryen da gwamnatinsa ke aiwatarwa domin ƙarfafa al’umma ta hanyar Shirin Cigaban Al’umma (CDP).
Ya kuma yi kira ga al’umma da su ci gaba da kasancewa cikin alaka da shugabanninsu, tare da bayyana goyon bayansu ga jam’iyyar APC a zaɓen shekarar 2027.
Bayan ziyarar ta fadar hakimin, Gwamna Radda ya kuma gana da manyan masu ruwa da tsaki na Ƙaramar Hukumar Dandume, inda suka tattauna muhimman batutuwan siyasa, ci gaba da hanyoyin bunƙasa ƙaramar hukumar.

Source: Facebook
Manyan jami’an da suka halarci tarukan sun haɗa da Mataimakin Gwamna, Malam Faruk Lawal Jobe; Darakta Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓe, Arc. Ahmed Musa Dangiwa; Mataimakin Shugaban Kwamitin, Alhaji Mustapha Muhammad Inuwa.
Sauran sun hada da Sakataren Kwamitin, Abdullahi Aliyu Turaji; da Shugaban Ma’aikatan Gwamna, Hon. Abdulakadir Mamman Nasir, tare da sauran jami’an gwamnati, shugabannin jam’iyya da masu ruwa da tsaki.
Sakon Gwamna Radda kan kisan Masussuka
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya bayyana alhininsa kan kisan fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka.
Gwamna Radda ya bayyana Sheikh Masussuka a matsayin mai kira ga zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin mabiya addinai.
Asali: Legit.ng

