Dan Atiku Ya Kaddamar da Gagarumin Shiri don Tazarcen Tinubu a 2027

Dan Atiku Ya Kaddamar da Gagarumin Shiri don Tazarcen Tinubu a 2027

  • Abba Abubakar ya ƙaddamar da shirin tattara mutane miliyan biyu a shiyyoyin Najeriya shida domin yaƙin neman zaɓen Tinubu
  • Ƙungiyarsa ta HBTO za ta fara gangamin siyasa a Abuja, sannan ta kai shi jihar Rivers a makon farko na Nuwamba
  • Ƙungiyar ta kuma sanar da shirin samar da motocin haya na alfarma guda 10 domin rage matsalolin sufuri ga ’yan Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Abba Abubakar, ɗan tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, ya ƙaddamar da shirin tattara magoya baya a shiyyoyin Najeriya shida domin tallafa wa sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027.

Abba, wanda ya kafa kuma yake jagorantar ƙungiyar Haske Bola Tinubu Organisation (HBTO), ya bayyana shirin ne ranar Juma’a, 30 ga watan Oktoban 2026 a sakatariyar jam’iyyar APC ta ƙasa da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi Umrah a Saudiyya, ya bayyana addu'o'in da ya yi wa Najeriya

Dan Atiku ya goyi bayan Tinubu
Bola Tinubu a wajen yakin neman zaben APC a Kaduna Hoto: Stanley Kingsley Nkwocha
Source: Facebook

Ƙungiyar ta kasance wata kafa ta siyasa da ke tattara jama’a tare da nuna goyon baya ga Tinubu. Abba ya sauya sheƙa zuwa APC a baya, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Ƙungiyar Abba za ta tattara magoya baya

Da yake bayyana shirinsu na gaba, Abba ya ce HBTO na shirin fara wani babban gangamin siyasa a faɗin ƙasar nan.

Ya ce ƙungiyar za ta fara tattara mutane miliyan biyu a shiyyoyin Najeriya shida, inda za a fara gangamin daga birnin tarayya Abuja.

A cewarsa, ƙungiyar za ta fara da tallafa wa Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, wanda ta bayyana a matsayin muhimmin jagoran siyasa a tsarin tattara magoya bayanta.

Abba ya ce manufar hakan ita ce haɗa ƙarfi domin tabbatar da nasarar Tinubu a Abuja a zaɓen 2027.

Ya kuma bayyana cewa suna aiki tare da burin siyasa na ministan na ganin Tinubu ya samu nasara a Abuja da jihar Rivers a zaɓe mai zuwa.

Kara karanta wannan

2027: Ɗiyar Tinubu ta yi maganar da ka iya tsorata 'yan Najeriya kan Atiku da Peter Obi

An shirya babban gangami a jihar Rivers

Ɗan tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ƙara da cewa ƙungiyarsa na shirya wani gagarumin gangamin siyasa a jihar Rivers a makon farko na watan Nuwamba.

Ya ce tuni aka fara farfaɗo da tsarin ƙungiyar a matakai daban-daban, yayin da mambobinta ke gudanar da ayyuka a wurare daban-daban domin faɗaɗa tasirinta.

A cewarsa, shirin ba wai kawai tattara jama’a ko yin gangamin nuna ƙarfi ba ne, illa gina ƙungiyar magoya baya mai tsari da za ta iya mayar da goyon bayan siyasa zuwa ƙuri’u a lokacin zaɓe.

Ya ce HBTO na da niyyar kafa cibiyoyinta a dukkan shiyyoyin siyasar ƙasar, ƙarfafa rassanta na jihohi da shiyyoyi, tare da haɗa kai da masu ruwa da tsaki a cikin al’umma.

HBTO za ta samar da motocin sufuri 10

Baya ga gangamin siyasa, Abba ya sanar da cewa ƙungiyarsa za ta fara wani shiri na tallafa wa harkokin sufuri ta hanyar samar da motocin alfarma guda 10.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kawar da shakkun 'yan Najeriya, ya fadi dalilinsa na runtumo basussuka

Ya ce an tsara shirin ne domin rage matsalolin sufuri da sauƙaƙa wa ’yan Najeriya wahalar zirga-zirga a kullum.

A cewarsa, za a fara aiwatar da shirin a Babban Birnin Tarayya kafin a faɗaɗa shi zuwa sauran sassan ƙasar.

Abba ya ce goyon bayan shirin Renewed Hope na Shugaba Tinubu ya kamata ya kasance tare da ayyukan da za su inganta rayuwar jama’a, ba wai kalaman siyasa kawai ba.

Ya bayyana cewa ƙungiyarsa za ta ci gaba da haɗin gwiwa da sauran ƙungiyoyin siyasa masu ra’ayi iri ɗaya domin neman nasarar Tinubu a zaɓen 2027.

A ƙarshe, ya ce ra’ayin siyasa na mutum abu ne da ya danganci tunaninsa, lamirinsa da ’yancinsa na yanke shawara da kansa.

Dan Atiku ya yi shiri kan tazarcen Tinubu
Atiku Abubakar na jawabi a wajen taro Hoto: @atiku
Source: Twitter

An soki Atiku kan takara a 2027

A wani labarin kuma, kun ji cewa Alwan Hassan, ya yi kakkausar suka kan tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar.

Alwan Hassan ya bukaci Atiku ya janye daga takarar shugaban ƙasa ta 2027, yana mai cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasar ba shi da wani sabon abu da zai iya yi wa ’yan Najeriya, musamman mazauna Arewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng