Wata Sabuwa: Ana Zargin ba Obasanjo Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa a 1999 ba

Wata Sabuwa: Ana Zargin ba Obasanjo Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa a 1999 ba

  • Tsohon sakataren gwamnatin tarayyya, Cif Olu Falae ya yi ikirarin cewa shi ne ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a 1999, ba Olusegun Obasanjo ba ne
  • Falae, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa ya ce ya faɗi haka ne domin ƴan Najeriya su san gaskiyar yadda aka dawo mulkin dimokuraɗiyya
  • Ya ce tun daga zaɓen 1993 da MKO Abiola ya samu nasara, Najeriya ke fama da matsaloli wajen gudanar da sahihin zaɓe

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a 1999, Cif Olu Falae, ya ce shi ne ya ci zaɓen shugaban ƙasar da ya dawo da mulkin dimokuraɗiyya.

Cif Falae ya yi ikirarin cewa shi ne ya lashe zaɓen shugaban ƙasar da aka yi a 1999 da ƙuri'u mafi rinjaye, ba Olusegun Obasanjo ba.

Olu Falae da tsohon shugaban ƙasa, Obasanjo.
Olu Falae ya yi ikirarin cewa shi ne ya ci zaɓen shugaban ƙasa a 1999 Hoto: @Olusegun_Obj
Asali: Twitter

Ya bayyana haka a cikin shirin safe mai taken, 'Morning Show' na kafar talabijin ɗin Arise ranar Alhamis, 12 ga watan Yuni, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Olu Falae ya faɗi abin da ya faru a 1999

Olu Falae ya yi zargi cewa an juya sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na 1999 ne domin a hana shi nasara, kamar yadda Vanguard ta kawo.

A cewarsa, wani bincike da lauyansa, marigayi J.O.K. Ajayi ya gudanar a kan sakamakon zaɓen ya nuna cewa ya doke Obasanjo na jam’iyyar PDP da fiye da ƙuri’u miliyan ɗaya.

“Lauyana, marigayi Ciff JOK Ajayi, ya gaya min cewa na ci zaɓen da fiye da ƙuri’u miliyan guda bayan tantance alkaluman da aka bayyana,” in ji Falae.

Dalilin da ya sa Falae bai kai ƙara kotu ba

Sai dai duk da haka, Falae ya ce ba su kai ƙara kotu ba saboda suna son ganin Najeriya ta koma mulkin dimokuraɗiyya cikin kwanciyar hankali bayan dogon lokaci karkashin sojoji.

“Amma duk da haka muka yanke shawarar kada mu je kotu. Mafi mahimmanci a gare mu shi ne Najeriya ta koma dimokuraɗiyya cikin lumana bayan shekaru na mulkin soja,” in ji shi.
Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo.
Olu Falae ya yi ikirarin cewa murɗe masa zabe aka yi a 1999 Hoto: Olusegun Obasanjo
Asali: Getty Images

Me yasa aka ba Obasanjo nasara a 1999?

Wasu dai na ganin dai zaɓen 1999 tamkar yarjejeniya ce ta siyasa domin kwantar da hankalin yankin Kudu maso Yamma, musamman bayan soke zaɓen 12 ga Yuni, 1993 da ake ganin MKO Abiola ne ya ci.

“Mun sha matsin lamba a wancan lokacin kada mu tayar da ƙura. Mun sadaukar da kai ne domin dimokuraɗiyya ta dawo.
"Na amince da sakamakon a wancan lokacin, amma dole ne a faɗi gaskiya, ni ne na ci wannan zaɓe."
“Ba son zuciya ta sa nake wannan magana ba, gaskiya kawai nake faɗa. Najeriya na da hakkin ta san gaskiyar tarihi a kan farfadowar dimokuraɗiyyar da ake ta surutu a kai.”

- In ji Olu Falae.

Obasanjo ya gaɗi yadda Abacha ya kitsa kashe shi

A wani labarin, kun ji cewa tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya yi ikirarin cewa Marigayi Janar Sani Abacha ya kitsa kashe shi a baya.

Obasanjo ya bayyana cewa bayan kama shi tare da Janar Shehu Musa Yar’Adua da MKO Abiola, Abacha ya shirya yadda zau raba su da numfashi gaba ɗaya.

Tsohon shugaban ya ce ya tsira daga makircin Abacha a lokacin ne kawai saboda rahamar Allah, ba wai saboda ƙarfinsa ko wata dabara ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262