Siyasar Amurka
Shugaban Amurka ya samu tirjiya kan kokarin mamaye Gaza da fitar da Falasdinawa daga kasarsu ta asali. Kasashen sun ce Trump bai isa ya kori Falasdinu ba.
'Yan Najeriya da suka zamo bakin haure a Amurka sun ce suna buya a gida domin kaucewa kamun da shugaba Donald Trump ya sa a yi wa bakin haure a kasar.
Kotu a ƙasar Amurka ta yanke wa Sanata Bob Menendez hukuncin zaman gidan kaso na tsawon sheƙaru 11 bayan kama shi da laifin cin hanci da rashawa.
Farashin mai ya fadi bayan Trump ya kafawa Saudiyya da OPEC kahon zuka a kan su rage farashin. Ya kuma yi alkawarin sanya takunkumi kan Rasha da China.
Shugaban Amurka ya dakatar da tallafin lafiya na masu cutar HIV da ake turawa kasashen Afrika da kasashe masu tasowa. Dokar Trump za ta yi tasiri a Najeriya.
Dan majalisar Amurka, Andy Ogles ya bukaci a ba Donald Trump damar wucewa a wa'adi na uku domin kawo cigaba. Majalisa ta yi muhawara a kan lamarin.
Shugaban kasar Amurka ya yi kaca kace ga malamar coci da ta nemi ya yi afuwa ga bakin haure da masu sauya jinsi a Amurka. Ya yi wa Mariann Budde kaca kaca.
An kori Admiral Linda L. Fagan, mace ta farko da ta jagoranci wani reshe na rundunar sojin kasar Amurka a cikin sa'o'i 24 da rantsar da shugaba Trump.
Trump ya zama shugaban Amurka na 47. An rantsar da shi a gaban iyalinsa, ciki har da Barron, wanda Trump ya ce ya taimaka wajen samun kuri’un matasa.
Siyasar Amurka
Samu kari