A Karshe, Amurka Ta Samu Abin da Take Bukata daga Iran a Mashigar Ruwa ta Hormuz
- Iran ta sanar da bude mashigar ruwa ta Hormuz da duka jiragen dakon mai bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Labanon
- Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya ce mashigar za ta ci gaba da zama a bude har zuwa karshen wa'adin tsagaita wuta
- Wannan na zuwa ne yayin da kasashen Turai ke ci gaba da fadi tashin nemo masalaha kan rikicin mashigar ta Hormuz da ke Iran
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Iran - Bayan tsawon lokaci, Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bude mashigar ruwa ta Hormuz ga duka jiragen dakon kaya a yau Juma'a, 17 ga watan Afrilu, 2026.
Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ne ya bayyana hakan, inda ya sanar da cewa an bude mashigar ruwa ta Hormuz gaba daya ga dukkan jiragen ruwa saboda tsagaita wuta a Lebanon.

Kara karanta wannan
Iran ta kafe kan sharadin sulhu da Amurka, ta yi fatali da tsagaita wuta na wucin gadi

Source: Getty Images
Iran ta bude mashigar ruwa ta Hormuz
Araghchi ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X yau Juma'a, lamarin da ka iya samar da kwanciyar hankali a wannan mashiga mai matukar muhimmanci.
A cikin wani sako da ya fitar, Araghchi ya ce matakin da gwamnatin Iran ta dauka na bude mashigar ga kowa, ya yi daidai da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma.
Ministan ya kara da cewa duk jiragen kasuwanci za su iya wucewa ta mashigar cikin tsari da hukumomin jiragen ruwa na Iran suka tsara.
Dalilin Iran na bude mashigar Hormuz
Ya kara da cewa bude mashigar na da nasaba da kokarin tabbatar da zaman lafiya da saukaka harkokin kasuwanci a yankin, musamman a lokacin da ake kokarin kawo karshen duk wani tashin hankali.
Abbas Araghchi ya ce:
"Sakamakon cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Lebanon, muna sanar da bude mashigar Hormuz ga duka jiragen ruwa har zuwa karshen wa'adin tsagaita wuta.

Kara karanta wannan
Akwai matsala: Amurka ta aika sako mai zafi, ta kafa sharadin komawa yaki da Iran
"Jiragen ruwa za su ci gaba da zirga-zirga bisa tsarin yadda Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa da Kula da Teku ta Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta riga ta sanar.
Amurka na ci gaba da killace Iran
Sai dai a gefe guda, rahotanni sun nuna cewa Amurka na ci gaba da killace tashoshin jiragen ruwa na Iran, bayan da tattaunawar da aka yi a Pakistan ta rushe ba tare da cimma matsaya ba.
Wannan mataki na zuwa ne yayin da shugabannin kasashen Birtaniya da Faransa ke gudanar da taron yanar gizo domin tattauna hanyoyin dawo da zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar, musamman ganin barazanar da ake fuskanta.

Source: Getty Images
Sai dai a halin yanzu, Iran ta share hawayen wadannan kasashe da ma ita kanta Amurka, inda ta bude mashigar domin ci gaba da zirga-zirgar jiragen dakon mai kamar yadda aka saba.
Iran ta yi fatali da tsagaita wutar wucin gadi
A wani rahoton, kun ji cewa Iran ta ce ba za ta amince da tsagaita wuta na dan lokaci ba yayin da take zargin Amurka da Isra'ila na hararar ƙasashen shiyyar Gabas ta Tsakiya.
Mataimakin ministan harkokin wajen Iran, Saeed Khatibzadeh, ne ya bayyana hakan jim kadan bayan tsagaita wuta ta tsawon kwanaki 10 tsakanin Isra'ila da Lebanon.
Saeed Khatibzadeh ta ce wannan matsaya ta Iran na nuna bukatar samun zaman lafiya mai dorewa, ba wai dakatar da fada na dan lokaci ba.
Asali: Legit.ng
