Kutse a majalisa: Rayuka 4 sun salwanta, an damke magoya bayan Trump masu yawa

Kutse a majalisa: Rayuka 4 sun salwanta, an damke magoya bayan Trump masu yawa

- Mutum hudu sun mutu yayin da 'yan sanda suka kama wasu 52 daga cikin magoya bayan Trump

- Hakan ya faru ne sakamakon gagagrumar zanga-zanga da kuma kutsen da suka yi a majalisar kasar

- Tuni dai shugabannin duniya da masu fadi a ji suka dinga sukar lamarin tare da kiransa abun kunya

Rayuka hudu sun salwanta kuma an cafke mutane 52 sakamakon zanga-zangar da magoya bayan Shugaba Donald Trump suka tada a ranar Laraba, Arise TV ta ruwaito.

Babban dan sanda, Robert J. Conteee ya ce a yammacin Laraba, magoya bayan Donald Trump sun shiga majalisar da niyyar tabbatar da nasarar zababben shugaban kasa Joe Biden.

Bayan sa'o'i kadan da yin gagarumar zanga-zanga da ke kalubalantar kayen da Trump ya sha, magoya bayansa dauke da tutoci sun ture shingen farfajiyar majalisar kasar inda suka kutsa ciki yayin da ake yin taro na musamman.

KU KARANTA: Hukuncin kuskure: Za a biya wani mutum N3.7bn bayan kwashe shekaru 28 a gidan kurkuku

Kutse a majalisa: Rayuka 4 sun salwanta, an damke magoya bayan Trump masu yawa
Kutse a majalisa: Rayuka 4 sun salwanta, an damke magoya bayan Trump masu yawa. Hoto daga Getty Images
Asali: Getty Images

Wannan lamarin kuwa ya sanya kasashen duniya da masu ruwa da tsaki suka kalla lamarin a matsayin yunkurin juyin mulki.

Da yawa daga cikin shugabannin duniya sun kushe lamarin da ya auku sa'o'i kadan da suka gabata a kasar Washington.

Firayim ministan Boris Johnson ya kushe lamarin inda yace abun kunya ne kuma ya bukaci a mikawa Biden mulki cikin ruwan sanyi.

"Abun kunya ya faru a majalisar Amurka. An san Amurka da tsayawa damokaradiyya a duk fadin duniya don haka ya dace a mika mulki ta ruwan sanyi," Johnson ya wallafa a Twitter.

KU KARANTA: Bidiyon Kakan da ya kai jikonkinsa gwajin DNA, ya gano ba shi ya haifa mahaifinsu ba

A wani labari na daban, Reno Omokri ya yi martani a kan rushe otal din da gwamnatin jihar Kaduna tayi sakamakon zargin zama wurin da za a yi liyafar badalar da wasu samari suka shirya.

A makon da ya gabata ne rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta damke mashiryan wata liyafar badala yayin da gwamnatin jihar ta rushe inda ake zargin za a yi liyafar.

A yayin martani game da rushe ginin, Omokri ya ce kamata yayi gwamnatin jihar ta rushe gidan dan gwamnan jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng