Tattaunawar Sulhu tsakanin Amurka da Iran Ta Dawo Farko, An Ji Halin da Ake Ciki
- Tattaunawar sulhu tsakanin Amurka da Jamhuriyar musulunci ta Iran na nan a matakin farko, inda a yanzu ake kokarin shimfida ka’idoji
- Wata majiya daga Iran ce ta bayyana hakan bayan bude mashigar ruwa ta Hormuz da kuma tsagaita wuta a yakin Isra'i'a da Lebanon
- Majiyar ta ce duk da wannan ci gaba da aka samu tsakanin kasashen biyu, har yanzu kokarin sulhun da ake yi na nan a matakin farko
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Iran - Rahotanni daga kasar Musulunci ta Iran sun nuna har yanzu ba a je ko'ina ba a tattaunawar da kasar ta fara da Amurka domin cimma yarjejeniyar kawo karshen yaki.
Wata majiya daga Iran ta bayyana cewa matakai na gaba da za a dauka tsakanin Iran da Amurka za su mayar da hankali ne kan amincewa da tsarin yadda za a gudanar da tattaunawar, ba wai cimma yarjejeniya ta karshe ba.

Kara karanta wannan
Amurka ta cimma matsaya da Iran kan shirin kera makamim nukiliya, Trump ya yi bayani

Source: Getty Images
Halin da ake ciki a sulhun Amurka da Iran
A rahoton da tashar Al-Jazeera, majiyar ta ce har yanzu bangarorin biyu na kan matakin farko ne na tattaunawa, inda ake kokarin shimfida ka’idojin da za su jagoranci zaman sulhu.
Ta kuma bayyana cewa batun sarrafa sinadarin Uranium da kuma makomar sinadarin da aka riga aka sarrafa a Iran na daga cikin manyan batutuwan da za a tattauna a gaba.
Wannan batu na daga cikin muhimman abubuwan da ke haddasa sabani tsakanin Iran da Amurka a kokarin cimma yarjejeniya, cewar rahoton NBC News.
Sharuddai 10 da Iran ta gabatar
Tun da farko, Iran ta gabatar da wasu sharudda guda 10 domin fara tattaunawa, ciki har da halin da ake ciki a kasar Lebanon, wanda shi ma ke da alaka da rikicin yankin.
Yarjejeniyar da aka cimma ta tsagaita wuta na kwanaki 10 a Lebanon jiya Alhamis, ta zama wata alama da ke nuna an samu ci gaba a yunkurin sulhun Iran da Amurka.
A lokaci guda, majiyar ta ce an dauki wasu matakai na sassauta yanayin zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar Hormuz cikin kulawa da tsari, domin rage tashin hankali da dawo da kwanciyar hankali.
Tuni dai Iran ta sanar da bude mashigar ga kowane jirgin ruwa bayan tsagaita wuta a yakin Isra'i'a fa kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon.

Source: Getty Images
Ana matakin farko a zaman sulhu
Majiyar ta jaddada cewa duk da wadannan matakai, har yanzu ana kan matakin farko a tattaunawar ne, kuma ba a kai ga cimma yarjejeniya ta karshe ba.
Duk da haka dai ana ganin cewa wannan matakai na tsagaita wuta a Lebanon da bude mashigar Hormuz na iya zama muhimman tushe wajen samar da fahimta tsakanin bangarorin biyu kafin a ci gaba zuwa yarjejeniya mai dorewa.
Trump ya yi maganar shirin nukiliyar Iran
A wani rahoton, kun ji cewa Shugaba Donald Trump ya yi ikirarin cewa Iran ta amince ba za ta kera makamim nukiliya ba har abada.
Shugaban kasar ya kuma musanta rade-radin cewa Amurka ta amince za ta saki kadarorin Iran da suka kai darajar Dala biliyan 20,

Kara karanta wannan
Akwai matsala: Amurka ta aika sako mai zafi, ta kafa sharadin komawa yaki da Iran
Wannan na zuwa ne yayin da rahotanni daga bangarorin Amurka da Iran ke nuna cewa an kama hanyar cimma matsayar zaman lafiya a tsakanin kasashen.
Asali: Legit.ng
