Jarumar mata: Kamala Harris ta zama mace ta farko da ta zama shugaban kasar Amurka

Jarumar mata: Kamala Harris ta zama mace ta farko da ta zama shugaban kasar Amurka

  • Mataimakiyar shugabar Amurka, Kamala Harris, ta kafa tarihin zama shugabar Amurka ta farko mace a duniya
  • Hakan ya faru ne sakamakon tafiya neman lafiya da shugaba Joe Biden ya tafi kuma ya mika mulkin kasar hannun ta
  • Kamar yadda kundun tsarin mulkin kasar Amurka ya bayyana, ita ce ta zama mai karfin iko a dukkan fadin kasar

Mataimakiyar shugaban kasar Amurka, Kamala Harris ta kafa tarihi a yayin da ta zama mace ta farko a duniya da ta samu karfin ikon shugabancin kasar Amurka yayin da shugaban kasa Joe Biden ya tafi asibiti.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, a wata takarda da Jen Psaki, sakataren fadar shugaban kasan ya fitar, yace Joe Biden zai je asibiti ne domin duba lafiyarsa.

Kara karanta wannan

Akwai yiwuwar kasar Amurka ta garkamawa Najeriya takunkumin sayen kayan yaki

"Mataimakiyar shugaban kasan za ta dinga aiki daga ofishin ta da ke West Wing a cikin wannan lokacin."
Kamala Harris ta zama mace ta 1 da ta haye mulkin Amurka, Biden ya tafi neman lafiya
Kamala Harris ta zama mace ta 1 da ta haye mulkin Amurka, Biden ya tafi neman lafiya. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

An taba mika karfin ikon shugabancin kasa ga mataimakin shugaban kasa a baya yayin da shugaba George W. Bush lokacin da likitoci suka binciki hanjinsa a 2002 da 2007.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, an mika wannan karfin ikon ne kamar yadda kundun tsarin mulkin kasar ya tanadar, Psaki yace.

Tsohon shugaban kasar Amurka, Donald Trump mai shekaru 75 a duniya ya ki a yi masa allurar da zai yi kwanaki ba ya cikin hayyacinsa domin neman lafiya, saboda ba ya son mika wa mataimakinsa mulki.

Kamar yadda sakatariyar yada labarai ta Donald, Stephanie Grisham, ta wallafa a wani littafi da ta fitar.

Kamar yadda kundun tsarin mulkin Amurka ya bayyana, mataimakin shugaban kasa zai kasance mai karfin iko da kasar a yayin da shugaban kasa ba ya nan.

Kara karanta wannan

Kafa Ƙasar Biafra Da Oduduwa: Tsohon Mai Neman Takarar Shugaban Ƙasa Daga Arewa Ya Goyi Bayan Kanu da Igboho

Biden, wanda a ranar Asabar zai cika sdhekaru 79 a duniya, shi ne mutum mafi tsufa da ya taba hawa kujerar shugabancin kasar Amurka a tarihin Amurka.

Kamala Harris ita ce mace ta farko da ta zama shugaban kasar Amurka a tarihi.

Fallasa: Yadda ɗiyar Tinubu ta ƙwace mana kaya, rufe kasuwa kuma ta buƙaci N5m, Jami'i

A wani labari na daban, Shugabannin kasuwar Oyingbo da ke Legas sun bayar da karin bayani kan dalilin da yasa aka rufe kasuwar na tsawon makonni biyu ta bakin shugaban 'yan kasuwar, Folashade Tinubu-Ojo.

Premium Times ta ruwaito cewa, kasuwar Oyingbo fitacciyar kasuwa ce da ake siyar da kayan abinci a Legas da jihohi masu makwabtaka.

Bayan rufe kasuwar na tsawon makonni biyu, 'yan kasuwar a ranar Laraba sun fito zanga-zanga kan rashin adalcin da aka yi musu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel