Saraki Ya Jefi Gwamnatin Buhari da Zargi kan Fashin Offa, Ya Tona Gwamnan Kwara

Saraki Ya Jefi Gwamnatin Buhari da Zargi kan Fashin Offa, Ya Tona Gwamnan Kwara

  • Tsohon shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ya bayyana cewa tsohuwar gwamnatin Buhari ce ta shirya makarkashiyar fashin Offa
  • Saraki ya zargi gwamnan jihar Kwara da ƙoƙarin sake ta tada tsohon zargin domin kawar da hankalin jama'a daga gazawar gwamnatinsa
  • Hukumar DPP dai ta riga ta wanke Saraki a shekarar 2018 bayan gaza samun hujja a kansa, amma yanzu gwamnati ta sake maka Saraki a kotu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kwara – Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya fito fili ya musanta zargin da ake masa na da hannu a mummunan fashin banki da aka yi a garin Offa shekaru takwas da suka gabata.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Juma'a, 17 ga Afrilu, 2026, Saraki ya bayyana cewa wannan lamari makarkashiya ce ta siyasa da aka shirya tun lokacin gwamnatin tsohon shugaba Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Shari'a ta dawo sabuwa: Saraki da tsohon gwamnan Kwara za su gurfana a kotu kan fashin Offa

Bukola Saraki ya ce gwamnatin Buhari ta yi amfani da fashin Offa don kwace mulki daga hannunsu.
Tsohon shugaban majalisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki. Hoto: @bukolasaraki
Source: Twitter

Fashin Offa: Saraki ya zargi gwamnatin Buhari

Saraki ya yi zargin cewa wasu mutane daga jihar Kwara ne suka haɗa baki da gwamnatin tarayya a wancan lokacin domin amfani da fashin a matsayin makamin da za su ƙwace mulki daga hannun sa a zaɓen 2019, in ji rahoton The Guardian.

"Ina so jama'a su sani cewa ba ni da wata alaka ta nesa ko ta kusa da fashin da aka yi, ko ma wani nau'in ta'addanci. Gwamnatin Buhari, da wasu mutane a jihar Kwara, sun yi amfani da fashin Offa a matsayin makami na kwace mulki daga gare mu a 2019."

- Sanata Bukola Saraki.

Ya bayyana matakin da Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq ya ɗauka na neman sake gurfanar da shi a matsayin abin kunya ga tsarin shari'a.

Tsohon shugaban majalisar ya tunatar da jama'a cewa tun a shekarar 2018, ofishin babban lauyan gwamnatin tarayya ta hanyar daraktan gabatar da ƙara (DPP), ya fitar da rahotanni guda biyu da suka wanke shi.

Kara karanta wannan

Atiku ya kare kansa kan zargin cin hanci, ya tuna baya kan abin da Obasanjo ya yi maaa

Saraki ya dura kan gwamnan Kwara

Rahoton ya yi bayani dalla-dalla cewa bayan binciken ƴan sanda, ba a sami wata alaƙa tsakanin Saraki da waɗanda suka je fashin ko kuma wani laifi na kisan kai ba.

A cewar Saraki, Gwamna Abdulrazaq ya tada wannan maganar ne kawai bayan ya yi hira da gidan talabijin na Channels TV inda ya soki matsalar tsaro a jihar.

"Daga na yi hira da Channels TV, inda na yi magana game da matsalar tsaro a jihar, sai kawai gwamnan ya tashi daga barci, ya sake dawo da wadannan tuhume-tuhume marasa tushe a kan gwamnoni biyu da suka gabace shi."

- Bukola Saraki

Ya zargi gwamnan da ɓoye rahotannin DPP da suka wanke shi yayin da yake ƙoƙarin yaɗa labaran ƙarya a jaridun ƙasa domin kawai ya ɓata masa suna da kuma cin mutuncin sa a idon duniya.

Saraki ya zargi gwamnan Kwara da dawo da batun harin Offa don rufe gazawar gwamnatinsa ta fuskar tsaro.
Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq ya na rattaba hannu kan wasu takardu a Ilorin. Hoto: @RealAARahman
Source: Twitter

Abun da Saraki ke shiryawa gwamna

Saraki ya jaddada cewa lauyoyinsa na a shirye don fuskantar gwamnan a gaban kotu domin tabbatar da gaskiya, kamar yadda rahoton Punch ya nuna.

Kara karanta wannan

Bayan tafiyar jami'an Amurka, 'yan ta'adda sun tsara kai babban hari Abuja, Neja

Ya bayyana cewa gwamnan ya yi ƙoƙarin amfani da iyalan waɗanda fashin ya shafa domin su shigar da ƙarar a kansa, amma sun ƙi amincewa da hakan bayan sun fahimci manufarsa ta siyasa.

Daga ƙarshe, tsohon gwamnan ya gargaɗi Gwamna Abdulrazaq cewa amfani da rigar kariya ta ofishin gwamna domin cin mutuncin magabata wani babban kuskure ne wanda ke mayar da martabar ofishin gwamna baya.

An maka Saraki da Abdulfatah a kotu

Tun da fari, mun ruwaito cewa, Bukola Saraki, da tsohon gwamnan Kwara, Abdulfatai Ahmed, za su fuskanci sababbin tuhume-tuhume 20 a ranar 4 ga watan Yuni, 2026.

Tuhume-tuhumen sun shafi kisan kai, haɗin baki wajen aikata laifi, da sauran laifuffuka da gwamnatin Kwara ta shigar a kansu game da mummunan fashin bankin Offa na 2018.

Babban abin da gwamnatin jihar ta gina ƙararta a kai shi ne bayanan amsa laifi da rahotanni suka ce Ayo Akinnibosun ya yi, ɗaya daga cikin waɗanda aka yanke wa hukunci a fashin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com